Labarai

IBB Ga Buhari: Rashawa Ta Fi Yawaita A Lokacinka Fiye Da Mulkina

Daga Sulaiman Ibrahim,
Tsohon Shugaban Soji Ibrahim Babangida yace ya fi Shugaba Muhammadu Buhari yaki da cin hanci da rashawa.

Tsohon shugaban kasar ya fadi haka ne a wata hira da aka yi dashi da ARISE TV ranar Juma’a.

Ya ce mutanen da suka yi aiki a karkashinsa tsarkaka ne idan aka kwatanta da wadanda ke kan mulki a yanzu.

Shugaban mulkin sojin ya ce ya dakatar da gwamnan mulkin soja a zamanin sa kan almubazzaranci da N313,000, amma a yanzu wadanda suka sace biliyoyin Naira a halin yanzu suna gudanar da lamuran su cikin walwala.

Da aka tambaye shi ko ya yarda da wadanda suka ce gwamnatin sa cike ta ke da rashawa, Babangida ya ce, “Amma abin da ke faruwa yanzu ya fi muni …. Daga abin da na karanta, bincike, ina tsammanin mu tsarkaka ne idan aka kwatanta da abin da ke faruwa a karkashin mulkin dimokradiyya.

“Na kori wani gwamna saboda karkatar da abin da bai kai dubu dari uku da goma sha uku ba.

“A yau, wadanda suka sace biliyoyi, wasu suna cikin kotuna ana shari’a kuma duk da haka yanzu suna baje kolin su akan tituna. Wane ne ya fi yaki da cin hanci da rashawa? .. mu tsarkaka ne idan aka kwatanta da wadannan. ”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: