Addini

Hukuncin Shari’ar Musulunci Za A Bi Domin Yi Wa Wanda Ya Zagi Annabi, Inji Sarkin Musulmi.

Daga Comrade Musa Garba Augie
Sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abbakar III, ya bayyana damuwar sa tare da Allah-wadai na yiwa Annabin rahama Muhammad (S.A.W) mummunan batanci a jihar Sokoto dake Arewacin Najeriya.

Sarkin musulmi ya ce, “abun ya dame shi matuka kuma ba zai saurara ba har sai ya tabbatar an zartar da hukumcin da ya dace ga wanda ya yi batancin”

Sultan Muhammad Sa’ad Abbakar III, ya nemi matasa da sauran al’ummomi dake Sokoto dasu kwantar da hankalin su na yin zanga-zanga akai-akai don ganin an hukumta wanda ya yi laifin. Ya ce ko shakka babu dole ne a yi hukumci akan sa.

A ranar talata da ta gabata ne wani mutun mai suna Ismail Sani Isah daga jihar Sokoto ya saki wani kazamin batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W) a shafin shi na Facebook wanda hakan ne ya harzuka rayukan sakkwatawa na ganin dole sai an yi hukumci kan mutumen.

Al’ummomi a jihar Sokoto a ranar laraba sun gudanar da zanga-zanga a kofar gidan sarkin musulmi dake kan wurin Sokoto inda suke son ganin sarkin musulmi ya saka baki na ganin an hukumta wanda ya yi batanci ba tareda sassauci ko dubin cewa ba mai hankali bane kamar yadda dangin sa suka sanar.

Sai dai kuma mai martaba sarkin musulmi Sultan Sa’ad ya ce, sun saka baki kan lamarin wanda yanzu haka mutumen na hannun hukuma kuma a ranar litinin mai zuwa za’a gabatar dashi gaban kotu don yi masa hukumci.

Sarkin musulmi ya ce, duba da lamarin da dami rayuwar su zai sanya dole zasu tabbatar an kai mutumen gaban kotun musulunci don yi masa hukumci dai-dai yadda shari’ar musulunci ta tanada.

Mi Zaku Ce?

Jaridar Sokoto

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Check Also
Close
Back to top button
%d bloggers like this: