Labarai

Hukumar ‘Yan Sanda Ta Karrama Shugaban KAROTA, Dr Baffa Babba ‘Dan’agundi Da Lambar Yabo Ta Girmamawa

Daga Indabawa Aliyu Imam
Hukumar ‘yan sanda reshen jihar Kano ta karrama shugaban hukumomin Karota/C.P.C Dr Baffa Babba ‘Dan’agundi da lambar yabo ta girmamawa.

Hukumar ta mika wannan lambar yabo ne ta hannun jami’inta S.P Magaji Musa Majiya wanda ke kula da rundunar masu lura da zirga-zirgar ababawan hawa na rundunar ‘yan sandan jihar Kano ‘MTD’

Hukumar ta karrama Dr ‘Dan’agundi ne bisa kokari, kwazo da jajircewa kan ayyukansa, musamman wajen tsaftace tuki da masu ababen hawa a jihar Kano, da kuma jajircewarsa wajen dakile siye da siyarwar gurbatattun kayan masarufi a jihar Kano.

” Kullum ina alfahari da jin dadi idan na ga jami’an ‘yan sanda da na Karota na aiki kafada da kafada musamman a yayin gudanar da ayyukansu a titunan jihar Kano.” In ji S.P Majiya.

Da yake jawabi Dr ‘Dan’agundi ya yi godiya ga hukumar ‘yan sanda tare da jaddada jajircewa wajen gudanar da aiki don a gudu tare a tsira tare.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: