Labarai

Hukumar Soji Ta Nijeriya Ta Gargadi Masu Hana Motocin Abincin Zuwa Kudu

Daga Zuma Times Hausa

*Ku bari ko kuwa ku fuskanci fushin doka.

Hukumar Sojojin NIjeriya ta yi gargadi da kaukasar murya ga masu tare hanyar suna hana motoci kai abinci zuwa kudancin kasar nan.

A wani rahoton da Zuma Times Hausa ya samu daga Jaridar Thisday, ta buga, ta bayyana cewa a wani sanarwa da Direkta yada labarai bna sojoji, (Defence Information, DDI), Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya sanya wa hannu ta ce, in har masu yin haka ba su daina ba, za su fuskancin fushin doka.

In masu karatu za su iya tunawa, Zuma Times Hausa ya kawo maku labarin cewa kungiyar masu Motocin Abincin sun hana membobin su kai abinci Kasashen Kudu saboda kashe da ake yi tare da kona masu dukiya inda su ka bukaci gwamnati su biya su diyya ko su daina kai abincin can.

Don ganin sun tsaya kan wannan kudiri, suke tare hanya suna hana membobin nasu kai abinci wanda hakan ya jawo fushin hukumomi.
©Zuma Times Hausa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: