Hukumar kwastam ta jinjina ma wani babban jami’in hukumar kwastam da yayi watsi da tayin dala dubu dari hudu da ashirin ($420,000) kimanin naira miliyan dari da hamsin da biyu kenan, da aka bashi don shigowa da miyagun kwayoyi.
Jaridar Legit.ng ta ruwaito shugaban hukumar, Kanal Hamid Ali mai ritaya ne ya bayyana wannan jinjina yayin da bikin karin girma da hukumar ta shirya ma wannan jami’in kwastam mai tsoron Allah, mai suna Bashir Abubakar.
A shekarar data gabata ne wasu miyagun mutane suka shigo da sundukai guda arba’in da daya (41), dake makare da kiyagun kwayoyin Tramadol ta tashar jirgin ruwa na Apapa dake jahar Legas.
- Advertisement -
Sai dai bayan an kama kwayoyin sai yan kasuwan da suka shigo dasu suka nemi shugaban tashar jirgin ruwan, Kwanturola Bashir Abubakar tare da bashi cin hancin $420,000, kimanin N152,040,000 kenan da nufin ya sakar musu kayansu.
Amma Allah Yasa Bashir Abubakar mutum ne mai tsoron Allah, sai ya tsaya kai da fata yace ba zai karbi wadannan haramtattun kudade ba, kuma ba zai saki haramtattun kwayoyin ba sakamakon suna lalata rayuwar matasa, musamman matasan Arewa.
Wannan gaskiya da Bashir Abubakar ya nuna tasa shugaban hukumar kwastam, Hamid Ali, wanda shima yayi fice wajen gaskiya, rikon amana da tsoron Allah, ya kara ma Bashir girma daga mukamin kwanturola zuwa mataimakin kwanturolan kwastam.