Uncategorized

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta ce kawo yanzu ta samu biza sama da 1,420 ga maniyyatan jihar.

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta ce kawo yanzu ta samu biza sama da 1,420 ga maniyyatan jihar.

Shugaban hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar.

Wakilin Nasara Radio a jahar jigawa Muhammad Sa’idu Limawa ya rawaito cewar.

An sanya dukkan maniyyatan da suka kammala biyan kudin aikin hajjin su a cikin tsarin biza.

Sannan kuma nan ba da jimawa ba hukumar za ta raba jakunkuna masu nauyin kilogiram 8 da yunifom ga jami’an cibiyar domin rabawa ga maniyyata.

A cewar Umar Labbo za a kuma yi allurar rigakafi ga maniyyatan a hedikwatar hukumar da sauran cibiyoyin da aka kebe a jihar nan ba da jimawa ba.

Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kara da cewa hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta kammala duk wani shiri na jigilar maniyyatan cikin sauki.

Ahmed Labbo ya yi nuni da cewa, hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta baiwa kamfanin Azman Air jigilar alhazan Jihohin Jigawa da Kaduna da kuma tawagar sojojin kasar nan zuwa Saudiyya.

Don haka shugaban hukumar jin dadin Alhazan ya bukaci maniyyatan da su kasance jakadu nagari ga jihar ta jigawa da kasa baki daya a lokacin da suke kasa mai tsarki.

Ka zalik ya yabawa Gwamna Badaru Abubakar bisa goyon baya da hadin kai da ake baiwa hukumar domin gudanar da aikin cikin nasara.

About the author

habibjs

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.