Labarai

Hukumar Hajji Ta Nijeriya Ta Fitar Da Sabbin Tsare Tsare

Hukumar hajji ta kasa ta fitar da sabbin tsare tsare da maniyyata za su bi domin zuwa aikin Hajji.
Yanzu kowanne maniyyaci sai ya samu mai tsaya masa, wanda zai sa hannu a takardar sa ta neman zuwa hajji. Mai tsayawar zai iya kasancewa mai unguwa ko kuma wani babban jami’in gwwamnati wanda ke kan matakin albashi na 14 ko fiye da haka.
Bayan wannan hukumar ta yi sabbin tsare tsaren bayarda kudaden guzuri ga maniyyata. A karkashin sabon tsarin, za a na biyan kudaden ne a cikin asusun banki kai tsaye.
Kakakin hukumar Alhaji Uba Malam ya bayyana cewa sun yi wannan sauye sauye ne domin rage yawan mutanen da ke zuwa kasar Saudiyya su batawa Nijeriya suna.
Ya kara da cewa duk wanda zai tsaya wa maniyyaci sai ya tabbatar da cewa mutumin kirki ne.
Hukumomin jin dadin alhazai na jahohin Nijeriya dai sun sha alwashin ganin an yi nasarar gudanar da wadannan sabbin tsare tsare.