HUKUMAR EFCC TA CAFKE GAWURTACCEN MADAMFARI MAI INKSNATION

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Datti Assalafy

Jami’an hukumar EFCC sun samu nasaran cafke hatsabibin ‘dan damfara Omotade Sparks Amos wanda ya damfari talakawan Nigeria biliyoyin Naira da sunan kamfaninsa na yaudara INKSNATION.

Jami’an EFCC sun cafkeshi ne yau a garin Sokoto bayan da hukumar EFCC ta shelanta nemansa ruwa a jallo watannin baya, sai yanzu aka ganoshi a Sokoto.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 773

Ina wakilan INKSNATION wadanda sukayi ta zagin Datti Assalafiy tare da cin mutunci fa batanci saboda na ja hankalin ‘yan uwa su guji INSKNATION su karbi kudaden da suka biya don a musu rijista saboda damfara ne?, Alhamdulillah yau gashi gaskiya tayi halinta.

Wadanda suka zageni, suka ci mutuncina, suka min sharri da munafurci na yafe wa kowa, Allah Ya yafe mu gaba daya.

Wannan dan iskan madamfari ya cutar da ‘yan uwa talakawa Wallahi, sai da ya bari an shiga kulle a farkon bayyana cutar Coronavirus, abincin da talakawa zasu ci ya gagaresu, sai ya bijiro da INKSNATION ya dinga karbe wa talakawa kudi, musamman mutanen mu na Arewa.

 

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: