Hotunan Yadda `Yan Shi`a Suka Ziyarci Kiristoci A Cocinan Abuja, Bauchi, Kaduna Da Kano Don Taya Su Murnar Kirsimeti
Daga Bilya Hamza Dass
Al’ummar Kirista a fadin duniya a jiya suka yi bikin tunawa da ranar da aka haifi Annabi Isah, kamar haka nema a kasar nan inda suke haduwa a magami’oinsu domin karanta tarihi da bukuwan tunawar.
Mabiya Shi’a Almajiran Shaik Ibraheem Zakzaky sun ziyarci alummar Kirista a garuruwa Kaduna, Abuja da Bauchi domin taya su murnar bukukuwan kirsimeti na bana.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘Yan Shi’a mabiya Shaik Zakzaky sun ziyarce su a cocinan domin. Daya ke bayani lokacin ziyarar a Elim Church dake Yalwa a garin Bauchi a madadin masu ziyarar Malam Nasiru Hassan Yalwa ya bayyana cewa wannan ziyara suna yin ta ne domin kyautata alaka da tabbatar da zaman lafiya cikin al’umma.
Mahalarta cocin sun yi matukar farin ciki da ziyarar sun nuna godiyar su tare kalmomin godiya.