Daga Haji Shehu A Nijar
Hukumomi a Jamhuriyar Niger sun gudanar da bikin cikar Jamhuriyar shekaru 60 da samun ‘yancin kai daga Turawan Mulkin mallakar kasar Faransa, bikin ya gudana ne a garin Damagaram dake jihar Zinder.
Bikin ya samu halartar Shugaban kasar Naieriya Muhammadu Buhari da Shugabannin kasashen Guinea da Burkina Faso da kuma Sarakunan gargajiya daga Nijeriya.
Daga cikin Sarakunan gargajiyar da suka halarci bikin akwai, Sarkin Gombe Dr Abubakar Shehu Abubakar lll, Sarkin Gumel, Sarkin Machina, da sauran Sarakuna na ciki da wajen kasar Niger.
Jami’an tsaro daban-daban sun gudanar da fareti tare da nuna kayan yakin dake gwada karfin Soji da kasar ta Niger ke da shi.