Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da wasu daga cikin jami’an gwamnatinsa ranar Asabar a birnin Landan, inda ya shafe fiye da wata uku yana jinya.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda ya shafe fiye da wata uku yana jinya a Landan, ya gana da Ministan Yada Labaran kasar Lai Mohammed da wasu daga cikin jami’an gwamnatin kasar a ranar Asabar
Jami’an da suka kai wa shugaban ziyara har da masu mataimakansa kan harkokin sada yada labarai Malam Garba Shehu da Femi Adesina
Har ila yau, cikin akwai mataimakiyarsa ta musamman kan harkokin ‘yan Najeriya da ke zaune a kasashen ketare, Abike Dabiri-Erewa da kuma maitaimakamasa kan kafofin sadarwan zamani Lauretta Onochie
A makon jiya shugaban ya gana da Shugaban Cocin Ingila, Archbishop na Canterbury, Justin Welby
A watan jiya ne shugaban ya gana da wasu gwamnonin kasar da suka kai masa ziyara a Landan
Ciki gwamonin da ya gana da su a watan Yuli har da gwamnan jihar Kano da Zamfara da Borno da sauransu
Buhari yana cikin nishadi a wannan hoton
Source BBC Hausa
Hotuna: Buhari ya gana da jami'an gwamnatinsa a London

Add Comment