Hoton Wanda Ya Bada Motoci 200 Dan Kamfen Din Buhari

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kyautar motoci 200 don tazarcen Buhari: Ba Ganduje bane ya bayar, kalli mutumin daya bayar

An gano mutumin daya baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari kyautar motoci daidai har guda dari biyu don yakin neman sake zabensa karo na biyu a yayin zaben 2019, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Talla

Tun da fari dai an fara yamadidin cewa gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ne ya bada kyautar motocin ga Buhari saboda ya samu sauki a bahallatsar karbar cin hanci data dabaibaye shi, sai dai hadimin shugaba Buhari, Bashir Ahmad ya musanta haka.

Bashir ya bayyana gaskiyar wanda ya bada kyautar motocin ne a shafinsa na Twitter, inda yace duk masu watsa jita jitar wai Ganduje ne ya bada motocin karya suke yi, sa’annan yace Yakubu Gobir ne ya bada motocin.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Haka zalika shi kansa mai gayya mai aiki, Alhaji Yakubu Gobir ya tabbatar da maganar Bashir, inda yace tabbas shine ya bada motocin ba Ganduje ba, kuma ya bada motoci dari biyu ne don amfanin yakin neman zaben Buhari da Osinbajo a zaben 2019.

Yace “Ni dan asalin jahar Kwara ne, kwararren ma’aikacin gwamnati ne, dan kasuwa ne, kwararren mai ilimin kimiyyar hada magunguna ne, ina da iyali, ina da mata kuma cikakken dan siyasa ne ni.”Kamar yadda ya fadi a shafinsa na Twitter.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: