Assalamu alaikum masu sauraren mu yau muna tafe da hurarmu da matashin mawaki mai suna Nani Media Gusau, nasan wasunku sun sanshi wasu ko basu sanshi ba, ga dai yadda hirarmu ta kasance dashi:-
ArewaBlog:- Tarihin Mawakin Da Kuma Asalin Sunansa?
Nani:– Assalamu alaikum ni dai da farko sunana zaharadeen sani gusau amman mutane sun fi sanina da nani media gusau nayi primary da secrdary na a cikin gusau kuma nayi karatun alqurani kuma alhamllahi na sauke.
ArewaBlog:- Mai Yaja Hankalinka Ka Fara Waka Sannan Wace Shekara Ka Fara?
Nani:- Na fara a 2013 har yanxu sannan kuma abun da yaja hankalina gurin waka shi ne anje dani ne studio sai aka barni babu kwai sai na fara aikin wata waka mai suna fauxeeya wanda ta fita a garin gusau har nayi suna da ita to sai nace kawai bari in cigaba da waka wannan shi ne ya ja har na cigaba da waka.
ArewaBlog:- Shin Wace Wahala Kasha Wajan Wannan Harkar?
Nani:- Gaskiya na sha wahala gurin waka sosai ko gurin launi da kuma qafiya sun bani wahala sosai sai kafin akoyamin waka nasha wahala saboda zaman studio sai wanda bakasani ba ma sai ya taimakama kuma da ga karshe nazo kuma nayi suna a jahar zamfara.
ArewaBlog:- Me Kake Son Cima A Wannan Harkar?
Nani:- Abun da nake so in cimma buri na guda biyu ne, na farko shi ne sauran jahohi susani sannan biyu ina so manya manya mawaka mu fara dasu kuma gaskiya alhamllahi na fara samu.
ArewaBlog:- A Kashe Wace Shawara Zaka Bawa Yan Uwanka Mawaka?
Nani:- Shawarata anan ita ce duk abun da kasa araika ko zaka samu cigaba kuma mutun ya bar ganin shi kara min mawaki ne to walahi idan ka dage ka cigaba to allah zai taimakeka, dagewa da kuma jurewa da wahala da zaka sha,
Allah ya taimaki mawakan mu na arewa ga baki daya ameen.
Wannan Shine Karshen Yadda Hirar Tamu Ta Kasance.