Kannywood

Hausa Film Industry Ta Cika Shekara 27 Da Kafuwa

Gaba dai gaba dai, masana’ar industiri ta fina finan hausa awannan shekararne ta sami cika shekara 27 da kafuwa ajahar kano dama tsirarun wasu jahohi acikin kasa Najeriya. An sami cigaba sosai acikin da suka gabata.

Azantawarmu da Alasan Kwalli wanda akafi sani da bakin wake ya bayyana mana irin cigaban da aka samu acikin wadancan shekarun da kuma yanzu.
.
Acewar Alasan Kwalli: tabbas, industry munci gaba kuma jama’a shaidane akan haka. domin ko a fina finan idan aka kalli na shekarun baya za’aga da banbanci dana yanzu. mu dauki misala akan fim din Sawun Keke, fim ne da magabatanmu suka shirya fim din, a wancan lokacin ba’a sami kwarewa wajen gina labarin da kuma daukar hoton fim din, amma duk da haka ya yi kyau da amana. bayan awannan shekarun akaga ya dace a yi ma shi kwaskwarima yanda zai dace da zamani, shine aka canja ma shi suna ya koma ”Wani Hanin Ga Allah” wannan misalin yana nuna yanzu mun sami kayan aiki masu kyau fiye da shekarun baya.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.