Hattara Maza Masu Kwadayi: Ta Aika Jarababbun Maza Masu Yawa Lahira


0 291

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Yanzu haka rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fara farautar wata yarinya mai suna Fatima Abdullahi Tuge.

A ranar 22 ga watan Afrilu ne rundunar ‘yan sandan kasa Najeriya ta fara farautar Fatima Abdullahi Tuge tare kuma da alkawarin kyautar kudi N250,000 ga duk wanda ya gano mafakar ta ko ya yi sanadiyyar kama ta ya mikawa ‘yan sanda.

An gano cewa Fatima Abdullahi Tuge ‘yar asalin jihar Kaduna ce, kuma kwararriya ce wajen damfara da neman maza, duk namijin da yayi sakaci sha’awa ta debe shi ya kwanta da ita, to babu makawa kwanan sa yazo karshe domin za ta tsaface shi.

Majiyar mu ta ruwaito cewa Fatima Abdullahi Tuge ta dade tana yada labaran karya da batanci a kafar sada zumuntan Facebook akan duk wanda ta nemi amincewar sa yaki, daga cikin wadanda Fatima Tuge ta nemi su amince da ita suka ki amincewa harda Hon. Gudaji Kazaure inda shi ma daga karshe ta yi masa sharrin damfara.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

Lamarin da yasa Hon. Kazaure ya rika farautar Fatima Abdullahi Tuge da Bindiga zai harbe ta ta gudu jihar Lagos.

Ko a wannan makon ma Fatima Tuge ta sake yiwa wani bawan Allah mai suna Mustapha Suleiman sharrin damfara kana kuma ta nemi bata rayuwar sa da sihiri shi ma domin yaki amincewa da bukatar ta.

Tuni dai Lauyoyin Mustapha Suleiman sun aike da kwafin takardar karar Fatima Tuge ga Kwamishinan ‘yan sandan kasa reshen birnin tarayya Abuja da kuma jami’an tsaron farin kaya domin a kamo Fatima Tuge ta girbi abinda ta shuka.

Allah shi kyauta, ya kuma kare al’umma daga sharrin shedanun matan zamani.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.