Labarai

Hatsarin Mota Ya Lakume Rayukan ‘Yan Bautar Kasa Biyar

Mummunan haɗarin da ya afku jiya Laraba a babbar hanyar Abaji zuwa Kwali dake Babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, ya yi sanadiyar mutuwar alkalla Matasa masu yi wa ƙasa hidima guda biyar.

Babbar Daraktar yada labarai da Hulda da jama’a na hukumar ta NYSC, Adenike Adeyemi ta fitar da wata sanarwa Mai taken “Ranar Laraba Mai Muni ga iyalan hukumar NYSC” wato ” Black Wednesday for NYSC Family” a turan ce.

Ta ce, “Cikin jimami da baƙin ciki Darakta Janar, da daukacin hukumar NYSC ke jajanta wa, iyalan matasan dake shirin fara bautan ƙasa, da suka rasa rayukansu a haɗarin motan da ya auku, misalan karfe 2 na daren jiya, Laraba, 28 ga Yulin Shekarar 2021, a babban titin Abaji dake Kwali.” Inji sanarwar.

“Hakazalika Dirakta Janar da daukacin hukumar na jajantawa gwamnatin jihar Akwa Ibom da na Imo, kan wannan haɗarin da ya yi sanadiyar rasuwar matasan masuyiwa ƙasa hidima.”

Itama dai fadar Shugaban ƙasar Najeriya ta fitar da saƙon jajantawa ta bakin Femi Adesina mai Taimakawa Shugaban ƙasar ta fannin yad’a labarai, Inda tayi Ta’aziyya ga Iyayen masu bautar ƙasar.

Daga Zuma Times Hausa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: