Rahotanni daga jihar Bornon Najeriya na cewa akalla mutane 20 ne suka mutu sannan fiye da 30 suka samu munanan raunuka sakamakon wani harin kunar bakin wake a garin Konduga.
Harin dai wanda aka ce wasu mata ne guda uku suka kai harin a wata kasuwar sayar da raguna da ke unguwar Mandirari da yammacin ranar Talata.
An dai ce guda biyu daga cikin matan sun kai ga tayar da bama-baman da ke jikinsu, a inda jami’an tsaro suka harbe ta ukun kafin ta tayar da nata.
Matan dai sun kasu gida uku ne a bangarorin kasuwar daban-daban.
Har yanzu dai babu wata kungiya ko mutum da ya dauki alhakin kai wannan hari.
Sai dai kungiyar Boko Haram ta tsaurara kai irin wadannan hare-hare a ‘yan kwanakin nan.
Kuma hare-haren na zuwa ne a dai-dai lokacin da sojojin kasar suka sha yin ikrarin ganin bayan kungiyar.
Wasu majiyoyin sun tabbatar wa da BBC cewa da yammacin ranar Talata, wasu ‘yan kunar-bakin-waken sun tayar da bam a yankin Aridamari da ke cikin birnin Maiduguri, sai dai kuma harin bai shafi kowa ba, a inda ya tashi da su kuma suka mutu.
Add Comment