Addini

Haramun Ne Mace Ta Saka Abaya Irin Ta Wannan Zamani Ta Fita Waje

Daga Kamal A. Rufa’i Rawaiya
Dalilin da ya sa na ce haka shine, abu na farko ita abaya ta wannan zamani ba ta suturce jikin mace kamar yadda shari’a ta tanada, saboda tana nuna siffar jikin mace karara, tana nuna gaban mace, tana nuna bayan mace, tana nuna zubin halittar mace, kuma tana kara qawata gaban mace da bayanta da surar jikinta, ita kuma jallabiyar da Shari’ah ta yi umurni a saka ba irin wannan bace, domin ita waccan batada kwalliyya kuma Mai yalwa ce wato Mai fadi ce matuka, ita ce ake cewa jilbab.

To ko a nan kadai na tsaya hujja ta fito fili dogaro da wannan ayar dake cikin 👉 Suratul Al-Ahzab, Aya ta 59
Inda Allah Madaukakin Sarki yake cewa:-
*( يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ قُل لِّأَزْوَاجِكَ وَبَنَاتِكَ وَنِسَاءِ الْمُؤْمِنِينَ يُدْنِينَ عَلَيْهِنَّ مِن جَلَابِيبِهِنَّ ذَٰلِكَ أَدْنَىٰ أَن يُعْرَفْنَ فَلَا يُؤْذَيْنَ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا )*

Ya kai Annabi (SAW ) Ka cewa matan ka da ´ya´yanka mata da matan Muminai su sassauta mayafinsu kasa yadda zai rufe tufafin da ke a kansu gabadaya. Wancan ya fi sauki kar a gane su domin kada a cuce su. Kuma Allah Ya kasance Mai gafara, Mai Jin kai.

Sannan akwai Hadithin, Abdullahi bin mas’ud (r a) inda yake cewa:-
”Innal mar’atu auratun” lallai Ita mace Al’aurace, kenan koda kwalliyya kawai kika yi a fuska to haramun ne ki fita waje wasu su gani, dole sai kin saka nikab.

Abu na biyu shine Abaya tana dauke da kwalliyya da ado iri daban daban wanda yake kara fito da kyawun mace a fili, kuma gashi acikin Alqur’ani Mai girma Allah Madaukakin Sarki yayi hani ga mace ta bayyana adonta saiga muharramanta, acikin Suratul An-Noor, Aya ta 31
Allah Madaukakin Sarki yana cewa:-

*( وَقُل لِّلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنْهَا وَلْيَضْرِبْنَ بِخُمُرِهِنَّ عَلَىٰ جُيُوبِهِنَّ وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا لِبُعُولَتِهِنَّ أَوْ آبَائِهِنَّ أَوْ آبَاءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوْ أَبْنَائِهِنَّ أَوْ أَبْنَاءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوْ إِخْوَانِهِنَّ أَوْ بَنِي إِخْوَانِهِنَّ أَوْ بَنِي أَخَوَاتِهِنَّ أَوْ نِسَائِهِنَّ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُنَّ أَوِ التَّابِعِينَ غَيْرِ أُولِي الْإِرْبَةِ مِنَ الرِّجَالِ أَوِ الطِّفْلِ الَّذِينَ لَمْ يَظْهَرُوا عَلَىٰ عَوْرَاتِ النِّسَاءِ وَلَا يَضْرِبْنَ بِأَرْجُلِهِنَّ لِيُعْلَمَ مَا يُخْفِينَ مِن زِينَتِهِنَّ وَتُوبُوا إِلَى اللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَ الْمُؤْمِنُونَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ )*

Kuma ka ce wa muminai mata su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjojinsu kuma kada su bayyana kwalliyar su face abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su sauke mayafansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nuna kwalliyyar face ga mazansu ko ubanninsu ko ubannin mazansu, ko diyansu, ko diyan mazansu, ko ´yan´uwansu, ko diyan ´yan´uwansu mata, ko matan su, ko abin da hannayensu na dama suka mallaka, ko kuwa maza wayanda suke biyawo gidaje marasa sha’awar mata, ko jarirai wadanda. ba su tsinkaya a kan al´aurar mata. Kuma kada su yi duka da kafafunsu domin a san abin da suke boyewa daga kafarsu.Kuma ku tuba zuwa ga Allah gaba daya, ya ku muminai! Tsammaninku, ku sami babban rabo.

To a nan gashi karara Allah Madaukakin Sarki yana hana mace ta nuna adonta ga wadanda suke ba muharraman ta ba, sannan kuma gashi a cikin Suratul Al-Ahzab, Aya ta 36:
Allah Madaukakin Sarki yana cewa:-
*( وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ وَلَا مُؤْمِنَةٍ إِذَا قَضَى اللَّهُ وَرَسُولُهُ أَمْرًا أَن يَكُونَ لَهُمُ الْخِيَرَةُ مِنْ أَمْرِهِمْ وَمَن يَعْصِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا مُّبِينًا )*

Ba abinda yake yiyuwa bane ga mumini kuma haka ga mumina, a lokacin da Allah da Manzonsa Ya hukunta wani umurni, sai wani zabi daga al´amarin su ya kasance a gare su. Kuma wanda ya saba wa Allah da ManzonSa, to, ya bace, bacewa bayyananna.

To yanzu idan mace ta saka Abaya ta fita waje ko ta je sallar idi da ita shin ta suturce jikin ta ne, ko kuma ba ta bayyana adonta ba, kenan idan haka ne ta sabawa dukkanin ayoyin da muka kawo gashi kuma Allah yana cewa ba abinda yake yiyuwa bane ga mumini namiji ko mumina mace su ce suna da wani zabi akan hukuncin Allah Madaukakin Sarki, da wannan za mu gane ashe saka Abaya a fita da ita waje haramun ne, ba ya halatta.

Sannan indai ke ‘yar mutunci ce Wallahi ba za ki saka Abaya ki fito waje ba, indai kina kishin kan ki kuma kin san darajar kan ki ba zai taba yiyuwa ba a ce kin saka Abaya ki fita waje da ita ba, idan kuma kika saka kika fita waje to kin zama wakiliyar Shedan.

Amma kin ga a cikin gida kina iya sakawa ko a gidan mijinki, amma idan za ki fita waje da ita to dole saikin saka cikakken hijab kuma shi ma ba mai kwalliyya ba, ba karami ba, kuma ba sharashara ba, ba mai kama da tufafin maza ba, ba na alfahari ba, mai kauri, kuma yalwatacce, sannan kar a saka masa turare, ba mai kala mai jan hankali ba, saboda haka mata sai a kiyaye kar Abaya Challenge ya halakar da ku.

Allah ya sa mu dace.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: