Wasanni

Har Yanzu Ronaldo Bai Yanke Hukuncin Zama A Juventus Ba

advertisement

Rahotanni daga kasar Italy sun bayyana cewa dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Cristiano Ronaldo bai yanke shawarar zama ko kuma ci gaba da zama a kungiyar ba duk da cewa bai koma hutu ba.

Tuni aka fara rade radin cewa dan wasan yana son barin Juventus zuwa daya daga cikin kungiyoyin Manchester United ko kuma Paris Saint German sai dai har yanzu kungiyoyin basu kai tayin kudi ba.

A kwanakin baya ne daraktan kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Pavel Nedved, ya bayyana cewa har yanzu Cristiano Ronaldo bai bayyana wata alamar cewa zai bar kungiyar kwallon kafa ta Juventus ba, kuma suna sa ran dawowarsa bakin aiki nan gaba a wannan watan bayan y agama hutu sakamakon fafatawarsa a gasar cin kofin nahiyar turai na Euro 2020.

Pavel Nedved ya bayyana cewa kawo yanzu Cristiano yana can yana hutu, kuma babu wata alamar da dan wasan mai shekaru 36, wanda saura shekara daya kwantiraginsa da kungiyar ya kare ya bayyana musu da ke nuni da cewa zai bar kungiyar saboda haka suna fatan zai dawo hutu domin ya ci gaba da buga wasa a sabuwar kakar wasan da za’a fara a watan gobe.

Ana bayyana shakku a game da makomar dan wasan, bayan da suka kammala kakar wasa mai sarkakkiya, inda Juventus ta gaza lashe kofin Serie A bayan shekaru 9, aka kuma yi waje daga gasar zakarun nahiyar Turai a matakin kungiyoyi 16, sannan ta karkare kakar a matsayi nan hudu, kuma a rana ta karshe.

Nedved, wanda tsohon dan wasan kasar Czech Republic ne ya ce lallai Juventus ta yi murnar kammalawa a mataki na hudu a karshen kakar wasa fiye da yadda ta yi murnar lashe gasar Serie A tare da Maurizio Sarri a shekarar 2020 kuma hakan ya biyo bayan gazawar kungiyar a kakar data gabata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button