Kannywood

Har Yanzu Ina Nan A Kwankwasiyya Babu Inda Naje – Inji Mustapha Naburaska

Daga Salisu Magaji Fandalla’fih
Fitaccen dan wasan Hausa kuma mabiyin tafiyar Kwankwasiyya Mustapha Naburaska, ya ƙaryata raɗe-raɗin da ake a kansa cewa ya bar tafiyar Kwankwasiyya.

Jaridar AMINTACCIYA Ta rawaito cewa, Naburaska ya bayyana haka ne a shafin sa na Instagram, Inda ya nuna rashin jin daɗin sa game da masu alaƙanta Maganar da yai a Freedom Radio da cewa yabar Kwankwasiyya.

Naburaska ya bayyana cewa Sana’ata Daban haka ma Siyasa ta Daban yace Dan Haka Duk Wanda Yace Zai Taimaki Sana’a ta Nima Zan Taimaka Mashi Tashi.

A cewar Naburaska shifa baice ya fita daga Kwankwasiyya kai tsaye ba, yace Dan Haka Har Yanzu Ina Nan Babu Inda Naje.

Naburaska yace Na Godewa Allah
Kuma ina rokon Allah Yasa Mu Gama Lafiya.

@Jaridar Amintacciya
08/09/2021

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: