Labarai

Har yanzu Ganduje Bai Bani Kudin Da Kotu Tace Ya Bani Ba, Cewar Ja’afa Ja’afar

DAGA Muhammad Kwairi Waziri
Mawallafin jaridar daily Nigerian, Jaafar Jaafar, ya bayyana cewa, har zuwa yanzu gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, bai biyashi ko sisi ba daga tarar da kotu ta bashi umarni ba.

Kotu ta bawa Ganduje umarnin bawa dan jaridar dashi da kamfanin jaridar sa wanda tun aranan 6/7/2021, Alkalin babbar kotun jiha, jostis Suleiman Danmalam, ta umarci Ganduje ya biya kudi N400,000 ga Jaafar Jaafar.

Haka zalika N400,000 ga kamfanin jaridar Daily Nigerian, bisa bata musu lokaci a shari’ar da aka kasa tabbatar da hujjoji.

Dan jarida Jaafar Jaafar wanda yanzu haka yake can kasar Ingila, bisa samun barazana da rayuwarsa da yace yana fuskanta a Nigeria.

Sai Dai Ganduje ya bijirewa umarnin kotun bayan kwanaki 30 da yake hukunci, bai samu tuntuba koshi ko lauyansa daga gwamna akan wannan batu ba har yanzu.

Yace, Saboda haka ne ya sake bukatar kotu ta umarci Ganduje ya bada hakuri ta hanyar manyan gidajen jaridun kasa guda biyu.

Tun farko dai gwamnan Kano Ganduje ne ya shigar da Jaafar Jaafar da jaridar Daily Nigerian kara a gaban kotu, bisa zargin bata masa suna.

hakan ya samo asaline biyo bayan sakin wasu bidiyo da Jaafar Jaafar yayi a shekarar 2018, wanda aka ga Ganduje yana karbar kudade daga hannun yan kwangila, wanda ake zargin rashawa ce.

Sidai Ganduje ya kasa tabbatar da zargin bata masa suna, duk da dai rahotanni sun bayyana yadda Ganduje ya shigar da wata sabuwar kara daban akan Jaafar Jaafar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: