-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Har Yanzu Dai A Kan Shirin SPower Na Gwamnatin Jahar Katsina


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Har Yanzu Dai a Kan Shirin SPower na Gwamnatin Jahar Katsina……

Tun Bayanda Gwamnati ta Bayyana aniyarta ta Biyan kudin Allawus GA Maaikatan na Spower Aketa samun korafe korafe musamman ma bayanda aka Fara Biyan kudin a Cikin wannan satin.

Korafi na Farko da aka samu shine anayin Table Payment Maimakon Direct ta Asusun Ajiyar bankunan Maaikatan Wanda Hakan Yana cigaba da samun Suka, duk kuwa da cewa Bayanai sun fito cewa:

Dalilin yin Hakan shine Dan a Tantanche a chire wasu da ake zargi Suna karkashin Shirin Npower na Gwamnatin Tarayya Kamar yadda aka Bayyana.

Koke na Bayabayan nan ya fito NE daga yankin Funtua Musamman Karamar Hukumar Kankara, Funtua Dama Faskari, Inda koke koken suke nuni da cewa akwai Alamun wakilan da Gwamnati ta Tura Suna aikata son rai.

Wani daga Cikin Maaikatan na Spower ya Bayyana cewa An Karbema dayawa takardasu ta offer a lokachin da sukaje domin a tantanchesu, Inda Akache masu Diplomar su bata bangaren Ilimi bace Dan haka Basu chanchanchi Shiga wannan tsarin ba, Abun Tambaya ana shine wannan Shirin anyishi NE ta kafar Internet Kuma aka Kirawo mutane aka tantanchesu tayaya baa gane duk wannnan ba sai yanzu Bayan Sunyi Aikin watanni Biyar wasu Kuma Hudu, sai yanzu da sukazo ansar Alawus Dinsu Agaya masu wannan, Muna Kira da Mai Girma Gwamna ya binchiki wannan Dan Allah.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 656

- Advertisement -

Haka nan bayanda aka kwachema wasu offer Akan cewa ba Fanni education suke ba duk da Hakan Kuma akwai wasu da aka Bari wadanda suma ba Fannin education din garesu ba kenan akwai Alamar tambaya?

Wani Korafin Kuma shine a Bayanin Gwamna yace duk Wanda yayi wata Hudu a biyashi Naira Dubu Tamanin #80,000 Wanda yayi wata ukku a biyashi dai dai lokachinda yayi Aiki, sai dai Alamu Suna nuni dacewa ana Biyan mutane kasada abinda yadache a basu Kuma a takardar sa Hannu Suna sa Hannu NE dacewa Dubu Tamanin din aka Basu shin tayaya zaa gane wadanda aka Ragema kudin?

Bayanda wasu sukayi Korafi Akan Hakan an Bayyana masu cewa wai anyi Amfani da reporting letters Nasu NE akabiyasu, Hakan Yasa wasu yin bore musamman a Karamar hukumar funtua inda daga bisani aka biyasu Kamar yadda tsarin take, Koma dai ya ta kasanche akwai bukatar Gwamnati tayi Duban tsanaki Akan wannan Lamarin.

Allah Yasa Adalin Gwamna yayi duba Akan koken wadannan bayin Allahn domin sun wahala musamman wadanda aka kwachema offers Dinsu Kuma baa biyasu hakkokinsu ba.

Muhammad Aminu Kabir
23112018

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: