Kannywood

Har Yanzu Bamu Daina Yiwa Ibro Addu'a Ba – Inji Bosho

Jarumi Sulaiman Bosho yana daya daga jerin wanda sukayi rashin marigayi Rabilu Musa Ibro.
Mutuwar Ibro ta doki jarumai masu tarin yawa, amma Sulaiman Bosho, Malam Dare, da Rab’u Daushe sune wanda afili akaga mutuwar tafi dagaza su.
 
A hirar da gidan Radio Kano ya yi da jarumi Sulaiman Bosho bayyanawa duniya cewa har yanzu bai daina tunanin marigayi Ibro ba. duk ranar daya tuna shi sai yaji aransa kamar alokacin ya rasu.
Acewar Bosho: Tabbas, mutuwar ibro ba zamu iya mantawa da itaba. dan haka har yanzu muna yi ma shi addu’a. kuma muna fatan Allah yaji kan shi.