Har kullum ina nadamar shiga APC, ku yi hakuri – Atiku ya roki yafiyar ‘yan Nijeriya
Atiku Abubakar, ya roki ‘yan Nigeria yafiya akan shiga cikin kungiyoin da suka hadu suka samar da jam’iyya mai mulki ta APC.
Ya ce rokon yafiyar ya zama wajibi duba da irin mawiyacin halin da ‘yan Nigeria suka shiga a cikin shekaru 3 da rabi da jam’iyyar ta kwashe.
- Advertisement -
Atiku, ya bayyana APC a matsayin wata matattarar wasu mugayen mutane da suka hadu waje daya don damfarar kasar Tsohon mataimakin shugabam kasa kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya roki ‘yan Nigeria yafiya akan shiga cikin kungiyoin da suka hadu suka samar da jam’iyya mai mulki ta APC.
Ya ce rokon yafiyar ya zama wajibi duba da irin mawiyacin halin da ‘yan Nigeria suka shiga sakamakon wannan majar a cikin shekaru 3 da rabi da jam’iyyar ta kwashe, kuma ya taka gagarumar rawa wajen ganin nasarar APC a 2015.
Atiku, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Yola, jihar Adamawa, a wani taron jin ra’ayoyin jama’ar garin Jimeta, ya bayyana APC a matsayin wata matattarar wasu mugayen mutane da suka hadu waje daya don damfarar kasar.