-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Hanyoyi Goma Da Za a Bi Ayi Za6en Gwamna Lafiya A Jihar Kano


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Comrade M.K Soron dinki

Babbar hanyar da ake bi wajen samun zaman lafiya a komai shine hadin kan mutanen da suke fada ko hamayya da junansu. Wannan hanyar itace mai sauki wajen wanzar da zaman lafiya, dole ne sai an samu hadin kai daga kowane bangare na masu hamayya sannan za a iya kore duk wani abu da zai iya kawo tashin hankali. Babu wani mabiyin wata tafiya, da zai iya daga kara a lokacin da shugabanninsa suka aminta da wata yarjejeniya. Yarjejeniyar ta wuce matsayin a rubutata kawai, bayan anyi rubutun dole za a yi aiki da abun da aka rubuta.

Idan har ana neman zabe na nutsuwa a jihar yakamata a tabbatar da wadannan abubuwan :-

1. Sai kowane bangare ya daina yin kalaman tinzirawa ga mabiyansa.

2. Tabbas sai ‘yan Kwankwasiyya da Gandujiyya sun ajje zafin kai a gefe.

3. Sai shugabannin kowane bangare sun fadakar da magoya bayansu akan zaman lafiya.

4. Kowane ‘dan siyasa sai ya yadda da ci ko faduwar za6e.

5. Sai ‘ya’yan talakawa sun dawo hayyacinsu, sun daina siyar da rayuwarsu ga wasu.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 25

- Advertisement -

6. Dole sai manyan gari da malamai sun tashi tsaye wajen nasiha ga ‘yan siyasa.

7. Dole ne sai an bar hukumar zabe tayi aikinta a matsayin hukuma mai zaman kanta.

8. Yakamata hukumar ‘yan sanda tayi aiki tuquru wajen yaqi da siyasar daba a ranar zabe kamar yadda muka ga sun fara.

9. Duk wani uba da manyan gari a jihar Kano sai ya fadakar da matasan yankinsa.

10. Sai kowa yayi biyayya ga dokokin zabe da na kasa baki daya.

Insha Allah yin hakan zai samar da zaman lafiya a zaben da za ayi na gwauna a Kano da ragowar jihohin Najeriya baki daya.

Allah yasa mu ga alheri.

#mikiya

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: