Nasiha

HANYOYI 15 DA ZAKA SA MATAR KA CIKIN FARIN CIKI


HANYOYI 15 DA ZAKA SA MATAR KA CIKIN FARIN CIKI:
1- Idan ka shiga gidan kace Assalamualaikum’ shaaidan zai bar gidan!
2- Ka rika yawan bata labarai.
Saboda Allah (S.w.t) ya sanar da mu
dan Adam yana son labari.
3- Ka zama mai yawan yabonta, musamman a wajen da ake kusheta
ka nuna 6acin ranka.
4- Ka zama mai yawan bata kyaututtuka. Kyauta tana kara dankon soyayya.
5- Ka share wasu daga cikin kuskurenta.
Ka nuna baka ma san ta yi ba.
Kuma ka dauka a matsayin abinda ya
shude, karka ajiye shi a kwakwalwarka.
6- Ka nuna mata tausayawarka gareta
a fili, musamman a lokacin da take
da juna biyu ko take jinin al’ada.
7- Kada ka daukaka abokanka fiye da matarka. (lokuta da dama wasu mazan
suna fifita abokansu na karatu ko na sana,a sama da matansu)
8- Ka nuna mata babu wata budurwa
dake gabanka sai ita, Ka nuna mata
kullum a matsayin sabuwa take a gurinka.
9- Ka rika tunawa da ita a cikin addu’arka. Hakan zai kara kauna tsakaninku.
10- Kada ka nuna mata ce wa kana yi mata alfarma akan wani kyatayi da
kake mata, kamar siyan abinci,Saboda daman hakkinta ne ka kawo mata,sannan kasan ce wa abincin kawai kake kawowa amma Allah shi ne mai ciyarwa.
11- Shaidan ne abokin gabarka ba matarka ba,Lokuta da dama idan mata da miji suka dan samu sa6ani har takai ana maida martani cikin fushi,To katuna ba daga ita bane shaaidan ne ke zugata, Saboda shi yana mutukar son ayi saki.
12- Ka dauki abinci ka saka mata abaki.
Annabi (s.a.w) ya ce, “abincin ba cikinta
kadai zai shiga ba, zai huce har zuwa zuciyarta.”
13- Ka kasance mai yawan yi mata murmushi/fara’a domin Manzo (s.a.w)
ya ce: “Duk wanda ya nunawa matarsa
fara’arsa to dai-dai yake da yin sadaka.”
14- Ka zama mai yawan neman shawararta.
(wasu suna ce wa ba,a shawara da mata). To ku sani ce wa manzo (s.a.w) ya kasance yana shawara da matansa.
15- Kar ka 6oye mata damuwar ka,
farin cikinka ko bakin cikinka.
Domin ita magani ce a tattare dakai.
Rubutawa :
Haiman Khan Raees 
@HaimanRaees

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.