Labarai

A hanyar Kano zuwa Daura Aka binne Sihirin Da Akayiwa Buhari

A HANYAR KANO ZUWA DAURA AKA BINNE SIHIRIN DA AKAWA Muhammadu Buhari – Aliyu A Jibia

Wani shehin malamin jamia mai suna Aliyu Jibia ya bayana a shafinsa na facebook cewa hakika yana da masaniyar cewa sihiri akawa shugaban kasa Muhammadu Buhari.

 

Ya kara da cewa a kasar Niger aka yo sihirin kuma aka binneshi a hanyar Kano zuwa Daura.

Malamin ya bayyana hakane a shafinsa inda yace wannan shine amsar da yaba shafin Mikiya.

Ya kara da cewa shine na Farko wajen Sanarda duniya tun a shekarar 2016 amma ba Wanda ya damu da abubuwan da ya tsinkayo.

A cewar Jibia “Ko rubutu na da Na yi Akan Bamagujen Dan Boko ai duk nuni ne Akan Wadanda ke kewaye da Buhari. Kuma sihirin a kasar Niger aka yi shi, amma a hanyar Kano zuwa Daura aka binneshi”.

Ya kara da cewa “Na yi matukar kokari na aikawa Maigirma Shugaban kasa da gudunmawa don warware sihirin ta hanyoyin makusantansa, amma bai je gareshi ba. A karshe, Na gaji, Kuma Na hakura”.

 

Mun Samu Wannan A Shafin Nigerian Dan Arewa a facebook

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.