HAKIKA WANNAN MUTUMIN ABIN KOYI NE.
A Wani gari, anyi wani kasurgumin Barawo. Shi wannan Barawon ya gallabi duk mutanen wannan garin da sata an kuma rasa yadda za’a yi da shi. Wannan Barawon yana da wata baiwa da Allah Ya yi masa, Allah Ya hore masa baiwar gudu kamar Barewa, in ya fita a guje, babu mai iya kama shi. Hakan Ta Sa lokuta da dama yakan yiwa mutane kwace sannan ya ce in ka isa ka biyo shi ka karba, dole mutum ko yaki ko ya so ya hakura don duk iya gudun mutum ya fi shi. Wata rana, wasu bayin Allah suna noman kwadago a gonar wani mutum, sai wannan Barawo ya je gonar da suke aiki. Ya kuwa tadda sunyi aiki sun gaji sun zauna suna cin abinci. Kawai Barawon yana zuwa sai ya dauki garmar daya daga cikin Ma’aikatan nan ya ja tinga ya tsaya ya ce : Na waye wannan? Sai wani daga cikin su ya ce tasa ce. Sai Barawon nan ya ce ” To in Ka isa ka biyoni ka amsa. To a wannan lokaci sai ya zamana shi mutumin da wannan Barawo ya daukarwa garma bashi da ko sisi, gashi Saura Sati daya a Daurawa diyarsa aure, bugu da kari matarsa bata da lafiya kuma ita wannan garmar Ita kenan ya Mallaka, domin da ita ya ke neman abinda zai ci da iyalansa. Ko da ya ji abin da barawon nan ya ce, sai ya juya ya cewa abokan aikin sa : ” To in kun je gida ku sanarwa iyalai na abinda ya faru, kuma ku fadawa mata ta cewa ta yafe min dukkan laifin da na yi mata ni kam na yafe mata tare da diyar mu. Sannan ku gaya wa Makwabci na Lado cewa a daura auren ‘Yata ko bani nan domin yau ko zamu kai bangon duniya, kuma ko zan mutu sai na kwato garma ta a hannun wannan barawon”. Yana gama fadin hakan kawai sai aka ga yana nade kamar Wando Alamar dai da gaske yake yi. Da ganin hakan sai Shi kuma wannan barawon jikin sa yayi sanyi ya aje garmar ya bar wurin. Lallai ya kamata mutane muyi koyi da wannan mutumin, a duk lokacin da muka sa wani abu a gaban mu, matukar dai mun san gaskiya ce tattare da wannan abun, to kada mu bar wani abu ko menene shi ya hana mu aikata shi.
Rubutawa
Haiman Khan Raees
@HaimanRaees
Add Comment