Labarai

HAJJIN BANA: Maniyyata Masu Zuwa Hajji Karo Na Uku Za Su Biya Karin Kudi Saudi Riyal 2000

HAJJIN BANA: Maniyyata Masu Zuwa Hajji Karo Na Uku Za Su Biya Karin Kudi Saudi Riyal 2000.

Daga Ibrahin Baba Suleiman.

Maniyyata Hajjin Bana wadanda za su maimaita hajji a karo na uku ko fiye a bana zasu biya karin kudin saudiyya riyal 2000 wanda yayi kwatankwacin kudin Nijeriya Naira 240,000.

In anyi chanji a Naira dari da ashirin riyal.

Wannan mataki an dauke shi ne saboda karawa wadanda wannan karon ne zuwan su aikin hajji kwarin guiwa.

 

Mahajjata da sukayi aikin hajji a shekarar 2014, 2015 da kuma 2016 kuma suna so suyi aikin hajji wannan shekara ta 2017 ko kuma nan gaba zasu biya wannan karin kudi.

Gwamnatin Saudiyya ta dau makamancin wannan mataki akan Umrah.

Gwamnatin Saudiyya a shekarar da ta gabata ta sanya wannan ka’ida ga Alhazan da suka gabatar da Umrah a shekarar a karo na uku ko fiye.

Dalilin wannan mataki shine rage yawan sauri a kan watannin Rajab, Shaaban, da Ramadaan.

Amma mafi tasirin dalili shine bawa wadanda basu taba ziyartan kasa mai tsarki ba cikakken dama.

Wannan tsari kuwa ya fara aiki cikin wannan shekara. Saboda haka wadanda sukayi aikin hajji sama da sau uku kuma zasuyi bana zasu biya wannan karin kudi saudi Riyal 2000, A kudin Naijeriya kuma N240,000.

Wannan doka ta shafi duk wata kasar da Alhazan ta zasu shiga kasar saudiya. Za’a iya biyan kudin ne ga wanda yaga zai iya a wurin hukumar Alhazai ko kuma kai tsaye ga hukumomin Saudiyya yayin da zasu karbi fasfo din mahajjaci bayan isar sa kasar.

Tuni dai wasu maniyyatan suka shirya wa wannan, wasu kuma suka hakura, amma manufar tsarin shine rage yawan maimaita aikin Hajji kowane shekara.

Allah ya bada ikon aikin Hajji karbabbe. Amin

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement