Labarai

An Haifi Jariri Da Hanjinsa A Waje A Jihar Neja

AL’AJABI

An Haifi Jariri Da Hanjinsa A Waje A Jihar Neja

An haifi wani yaro da kayan cikin sa a waje a babban asibitin garin Kontagora dake Jihar Neja, amma likitocin asibitin na Kontagora sun tura yaron zuwa asibitin kwararru na Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Specialist) dake Minna babban birnin jihar ta Neja domin yi masa aiki.

Wani Attajiri mai suna Alhaji Abdulrahman MK dake garin na Kontagora ne ya dauki nauyin yi masa aiki.

Kawo izuwa yanzu likitoci sun yi wa yaron aiki inda ake ci gaba da jinyarsa.

Daga Kwamared Zakari Y. Adamu Kontagora

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: