Hausa Films Kannywood

Hadiza Gabon Ta Name Gafarar Allah  

Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood Hadiza Gabon ta roki Allah gafara kan wata “katobara” da ta ce ta yi da na sanin yin ta a shafin Twitter ranar Lahadi.

Tun da fari dai Gabon ta mayar wa wani mutum martani ne a shafin Twitter wanda ya zage ta a wani hotonta da na kawayenta kuma abokan aikinta Rahama Sadau da Fati Washa da Rahaman ta wallafa a Twitter.

Hoton dai ya jawo ce-ce-ku ce a shafukan sada zumunta musamman na Twitter da Instagram inda dukkan jaruman suka sanya a shafukansu.

Wani matashi ne ya fara cin zarafin jaruman inda ya zarge su da yin zina kafin su dauki hoton. Ba da jimawa ba ne ita kuma Hadizan ta mayar masa da martani da cewa da mahifinsa ma suka yi zinar.

Tuni dai Hadiza ta goge wannan sako ta kuma wallafa wani na neman gararar Allah SWT da yin da na sanin mayar da wancan martanin tun da fari.

Sakon nata ya ce: “Astaghfirul Laah kan martanin da na mayar marar kyau kan wata amsar rashin da’a da wani ya ba ni. Na goge sakon kuma na nemi garafar Allah kan kokarin mayar da martani cikin fushi kan wani kuskuren da aka yi.”

Ta burge mutane har da Minista Pantami

Wannan abu da Hadiza ta yi dai ga dukkan alamu ya burge ma’abota shafukan sada zumunta da muhawara a Najeriya, inda daga wallafa sakon da misalin karfe 5.58 na yammacin Lahadi zuwa 9.30 na safiyar litinin an sake yada shi sau 638 an kuma so shi sau 3,600 sannan wadanda suka bayar da amsa ga sakon suna da dumbin yawa.

Za a iya cewa kashi 95 cikin 100 na wadanda suka ba da amsa sun yabe ta ne kan tuban da ta yi, amma duk da haka akwai ‘yan tsiraru da ke ganin cewa “aikin gama ya gama, ta makaro, abin da suke ganin ya nuna zahirin wace ce ita.”

Ministan Sadarwa na Najeriya kuma fitaccen malamin addini Sheikh Isa Ali Pnatmi ma ya bayar da amsa a kasan sakon Hadizan.

Sakon ministan dai na cewa ne “Wannan babban abun a yaba ne a nemi gafarar Allah bayan yin wani kuskure. Allah Madaukakin Sarki ya yafe mana ya kuma yi mana jagora tare da kare mu a gaba.”

Sai dai shi ma ministan ya sha martani daga wasu mabiya Twitter din inda wasu ke cewa me ya kawo shi cikin wannan maganar, yayin da wasu kuma ke yaba masa.

Ainihin hoton da ya jawo ce-ce-ku ce din

A ranar Asabar ne Rahama Sadau ta wallafa hoton mai dauke da ita da Hadiza Gabon da Fati Washa a shafin Twitter inda ta yi masa take da “ma ki gani ya kauda idonsa”.

Sannan ta sake wallafa irinsa a shafin Instagram inda kuma nan da nan hotunan kala uku suka yadu kamar wutar daji.

Sun dauki hoton ne a birnin Landan yayin da suka je karbar wata karramawa da aka yi musu.

Sun sha caccaka sakamakon sanya hoton inda aka dinga yi musu zargi iri-iri na zina da madigo, abin da ya tunzura Gabon mayar da “kakkasaun martanin” ga wani Bala Boyi.

Nan da nan ita ma Rahama ta sake sanya martani a kan na Gabon din.

Mutane da dama na ganin bai dace jaruman su yi haka ba, kamata ya yi su kau da ido kan irin wadannan zarge-zarge.

Daga baya ne a ranar Lahadi da yamma ita Hadizan ta goge martani tare da bayar da hakuri, sai dai duk da cewa ita ma Rahama ta goge nata martanin amma dai ba ta bayar da hakurin ba sannan ba ta cire hoton ba.

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement