Hadiza Gabon Ta Kusa Kurmanta Amina Amal Saboda Duka, Cewar Barista Uba


0 531

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Tun bayan da rikici ya barke tsakanin fitacciyar jaruma Hadiza Aliyu Gabon da Jaruma Amina Muhammad Amal a ke ta faman cece-kucen da ya dauki hankali, musamman bayan da a ka Jaruma Gabon ta bayyana hoton bidiyo ta na dukan Amal din tare da yi ma ta tambayoyi, lamarin da ya ja hankalin wasu lauyoyin kare hakkin bil adama su ka shigar da kara a gaban kotu, don nema wa karamar jarumar hakkinta.

A kwanakin baya LEADERSHIP A YAU ta ruwaito cewa, Amal ta kamu da rashin lafiya, inda ta yi jinya sakamakon wannan duka da a ka yi ma ta, to amma bayanai sun nuna cewa, bangaren Gabon su na zargin cewa, labarin kanzon kurege ne. To, amma a wannan tattaunawar da daya daga cikin lauyoyin da su ke tsayawa Amal, wato BARISTA NAZIR A. UBA, ya yi da LEADERSHIP A YAU ya tabbatar da rashin lafiyar, inda ya yi karin haske da cewa, har yanzu jarumar ta na fama da matsalar ji a kunnenta guda daya sakamakon wannan duka da ta sha.

Ga dai yadda tattaunawar ta kasance: Za mu so mu ji dalilin da ya sa ku ka shigo cikin wannan batu na neman hakki. To, kamar yadda na sha gaya wa mutane ’yan uwanku ’yan jaridu, Najeriya har yanzu ba ta yi lalacewar da mutum da zai yi laifi kuma ya san laifi ne ya dauka ya yi ‘posting’ ba ko da laifin nan kasa ya shafa gabadaya ko kuma a’a jiha ya shafa ko karamar hukuma ko kuma hakki ne na wani.

To, saboda haka bayan mun ga an ci zarafin wannan yarinya, an dake ta an zage ta, an yi ma ta kazafi a kan abinda ita an ce a na zargin ta cewa ta yi, amma kuma ita ba ta yi ba, kuma duk duniya babu wani ‘post’ da ya fita ko na magana ko na wani abu. Mu dai ba mu gan shi ba, ba mu ji shi ba, wanda ya jawo a ka yi wannan cin zarafi da a ka yi ma ta.

To, wannan shi ne dalilin da ya sa bayan abubuwan sun fita, wata kungiya a can Amerika ta ga cewa ya kamata a zo a shigar wa yarinyar nan, saboda a na tunanin fada ne tsakanin mai karfi da maras karfi ko kuma mai kudi da talaka ko kuma sa ‘superstar’ da wacce ba ‘superstar’ ba misali. Wato ku na ganin akwai cin zali kenan? Akwai cin zali cikakke a ciki.

To, shi ne kungiyar ta neme mu kuma yanzu kofarmu a bude ta ke, saboda kullum sai na amsa waya akalla 15 zuwa 20 na lauyoyi daban-daban maza da mata da kungiyoyi da su ke son su shigo cikin wannan tafiya a yi da su, saboda su kansu ’yan wannan masana’anta ta Kannywood gata a ke yi mu su, idan a ka zo a ka nemi hakkinta. Idan kotu ta gamsu da abinda mu ke fada, ta ga ta cancanta, da a bi ma ta hakkinta, shikenan.

Idan wannan kotu ta ce ba ta cancanta ba, to akwai kotuna a sama, za mu iya tafiya. Kuma wannan shi ne dalilin da ya sa mu ka shigo. Kenan ka na so ka gaya wa duniya cewa, ba Amal ce ta nemi ku shigo ku nema ma ta hakki ba, a’a, ku a matsayinku na masu kare hakkin bil adama ne su ka shigo? Magana ta gaskiya kafin wannan shari’ar, Amal saidai na gan ta a allon talabijin ko kuma na ga labaranta a Youtube ko a fim din Hausa. Ban taba ganin ta a fili ba, ba ni da ‘contact’ dinta kuma ba ita ta neme mu ba.

To, amma mutane za su so su san wacce kungiya ce daga Amerika ta neme ku ta ke daukar nauyin shari’ar. To, wannan kungiyar sun bukaci mu boye sunansu, amma idan lokaci ya yi, wanda ya kamata a sani, za a sani, kuma mun yi mu su ‘undertaking’ cewa ba za mu bayyana su ba, saboda har yanzu a shari’ance dai bayan ‘issue’ na shari’a da a ka buga a jarida ba a kai wa ita Gabon takardar kara ba, saboda a na cewa ba a yi ‘direction’ ba (wato tsayar da kotun da za ta yi shari’ar).

Saboda haka abinda mu ka sani shi ne mun shigar da kara, mu na jiran a yi ‘direction’ mu ji wacce kotu ce za ta yi, mu je mu dauki rana mu sadar da ita Gabon da sammaci. Kuma abinda kotu ta yi, shikenan. To, bayan kun shigo cikin lamarin, shin kun nemi amincewar ita Amal din a kan za ku tsaya ma ta? Eh, gaskiya mun yi wannan, kuma a rubuce ma ta yi, don kada a samu matsala ko tangarda ko kada wani ya zo ya zare ma ta idanu ko a nuna ma ta karfi ko wani abu ko wata yaudara, daga baya ta zo ta yi ‘disowning’ din mu, saboda an sha yin haka, shi ne mu ka sa ta rubuta takarda tun farko, wacce ita ce za ka ga ta na yawo, ta amince a lokaci lauyoyi 12 ne, ta amince a matsayin lauyoyinta. Amma an ce a na kokarin a sulhunta maganar nan. Gaskiya ne?

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 317

- Advertisement -

To, ka san har kullum shi sulhu alheri ne. Ko ba haka ba? Kuma kamar yadda na sha fada, a kowane mataki a shari’ance a na yin sulhu koda kuwa kotu ta yi hukunci za a iya zaunawa a yi sulhu tunda cikin yardar Allah a iya wannan mataki da a ke ciki na yanzu mun shigar da shari’ar neman hakki ne kawai kuma kawai yiwuwar za a sulhunta din, domin mun zauna ita uwar kungiyarsu (‘yan fim) ta MOPPAN mun fahimci juna. Mun yi magana da su cewa, za a zauna, idan sulhu ya yi, shikenan ba mu da damuwa.

To, ku na da wasu sharudda a wannan sulhu da za a yi? Eh to, sharuddanmu ai su ne da ma abinda ya sa mu ka garzaya kotu shi ne abinda a ka yiwa ita wannan yarinya da mu ka ga ba daidai ba ne, kuma mu ka roki kotu ta bi wa yarinyar nan hakkinta ta hanyar roko da mu ka yi a gabn kotu cewa ita Hadiza Gabon yakamata ta buga a manyan jaridu guda biyu wadanda a ke sayar da su a mataki a kasa cewa ta na neman afuwar Amal, sannan ta rubuta cewa da yawunta ita ko ta sa wasu ba za ta sake yi ba. Saboda ka san ba fa ita Hadiza Gabon kadai ce ta dake ta ba. Akwai sauran yaranta da direbobinta da duk wani wanda za ta iya ba wa umarni ya ji ko kuma ta hana shi ya hanu, ya taimaka wajen dukan wannan baiwar Allah.

To, amma a takardar da mu ka gani mun ga cewa ita Hadiza Gabon kadai ku ka kai kara, ba ku saka wadancan mutanen da ka ambata b  a. Wannan gaskiya ne, amma a shari’ance ba za ka kai mutumin da ba ka san shi ba kara. To, saboda haka idan mu ka sa sunan mutumin da ba mu sani ba, shari’ar tamu za ta iya samun tazgaro. Ita wannan (Hadiza) ita mu ka sani kuma duk abinda su ka yi da yawunta ne. To, saboda ha ka ita za mu iya sadarwa da sammaci kai-tsaye. Saboda haka wadancan mutane (a wajenmu) su na yi ne da yawunta.

To, ku kenan ku na nufin ko da a na cikin shari’ar ne idan ku ka gano akwai wane da wance a mutanen da a ka je da su a ka yi dukan, su ma za a shigar da su cikin shari’ar kenan? Eh to, wannan kuma sai abinda hali ya kama… A shari’ance hakan zai iya yiwuwa. Akwai tunanin hakan.

To, yanzu kun kai ga mika wa rundunar ’yan sanda koken ta yi bincike kuma ta shigar da caji baya ga wannan shari’ar da neman diyya? Eh, mu na shirin hakan sosai ma kuwa. Ba ku kai ga mikawa ba? Ba mu kai ga yin hakan ba, amma dai akwai hakan. Shirye-shirye sun yi nisa wajen yin hakan. To, amma akwai batun shakkun cewa, bidiyon da a ka gani ba a ga fuskar ita Hadiza Gabon ba, sai muryarta, wanda hakan ke nuna cewa watakila ma ba ita ba ce. Eh, akwai matakai sosai da sosai kuwa.

Ka san sha’ani na bincike shi zai bayyana. Idan ta (Hadiza) ta musa, to mun tanadi hanyoyi wasu daban, mu na nan da hujjoji a tare, wadanda za su tabbatar da cewa ita din ce. Wannan su na nan a shirye mun shirya su kuma cikin yardar Allah za mu gabatar da su a wajen ’yan sanda ko a wajen hukumar kula da cin zarafin mata da kananan yara ta kasa ko kuma ko ma a wajen wacce hukuma ce mu ka kai, domin su tantance su gani. Idan su ka ce sun gamsu, sai su dauki matakin da su ka ga ya dace.

A kwanakin baya an bayar da rahoton cewa, ita yarinyar nan Amal ta tsinci kanta a halin rashin lafiya. Shin meye gaskiyar wannan maganar? Wannan gaskiya ne, don lokacin da yarinyar nan ta zo Kano ma ta na cikin halin kaka-ni-ka-yi. Idan ta ci abinci, ta yi amai, a kara ma ta ruwa, a yi wane-a yi wane har ma mu ka fara tunanin ‘case’ din ma ba zai yiwu ba, saboda yanayin jikin. To, cikin yardar Allah dai jikin ya zo yau, gobe ya koma, amma dai alhamdulillahi yanzu babu matsala sosai, ta na iya yin magana, ta na iya cin abinci.

Amma har yanzu ta na cewa, ba ta ji a kunnenta guda daya; ko na hagu ko na dama, inda a ka dake ta da takalmi da sanda da sauran abubuwa, wanda idan hali ya yi duk za mu gabatar a gaban kotu cikin yardar Allah. Amma wasu su na son su san a wane asibiti a ka duba ta, saboda su na ganin kamar karya ne labarin da a ka buga na rashin lafiyar. Wannan idan hali ya yi duk za mu sanar, amma abu ne na bincike; ba ma so mu bayar da satar amsa a kai. Ka san shi yaki dan zamba ne.

To, zai yiwu gabadaya a ce duk shirye-shiryenmu ya zama mun yayatawa duniya ba. Amma idan hali ya yi za a san asibitin da su ka bincika su ka yi komai, domin akwai komai da komai an tanada, kuma cikin yardar za mu kawo gaban kotu.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.