Muna tafe da hadis din da yake bayani akan Abubuwan da aka gina musulunci akai
عَنْ أَبِي عَبْدِ الرَّحْمَنِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُمَرَ بْنِ الْخَطَّابِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ: سَمِعْت رَسُولَ اللَّهِ صلى الله عليه و سلم يَقُولُ: ” بُنِيَ الْإِسْلَامُ عَلَى خَمْسٍ: شَهَادَةِ أَنْ لَا إلَهَ إلَّا اللَّهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ، وَإِقَامِ الصَّلَاةِ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ، وَحَجِّ الْبَيْتِ، وَصَوْمِ رَمَضَانَ”.
[رَوَاهُ الْبُخَارِيُّ]
، [وَمُسْلِمٌ].
ALHADITHUT THALITHU (3)
An Abi Abdurrahmani Abdullahi bn Umara bin Al-khattabi (RA) Kala: sami’itu Rasulallahi (SAW) yaKuulu: “Buniyal Islaamu alaa khamsin: Shahadati an La’ilaha ilallahu wa’anna Muhammadan Rasulullahi, wa iKaamis-saalati wa’iita’iz zakaati, wa hajjil baiti, wa saumi Ramadana.
“Rawahul Bukhari wa Muslimun.
HADISI NA UKU (3)
An rawaito daga Abdullahi dan Umara dan Khattab (RA) ya ce: Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “An gina Musulunci a bisa bubuwa guda biyar:-
1-Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (da shaidawa) Annabi Muhammadu Manzonsa ne.
2-Tsai da sallah.
3-Ba da zakka.
4-Ziyarar dakin Allah Mai Girma.
5-Azumin watan Ramadana.
Buhari da Muslimu ne suka rawaito shi.
Daga Abubakar Salihu Kabara