Hadisi Na Hudu (4) -Arba`una Hadis

0 943

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

عَنْ أَبِي عَبْدِ الرَّحْمَنِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ مَسْعُودٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ: حَدَّثَنَا رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه و سلم -وَهُوَ الصَّادِقُ الْمَصْدُوقُ-: “إنَّ أَحَدَكُمْ يُجْمَعُ خَلْقُهُ فِي بَطْنِ أُمِّهِ أَرْبَعِينَ يَوْمًا نُطْفَةً، ثُمَّ يَكُونُ عَلَقَةً مِثْلَ ذَلِكَ، ثُمَّ يَكُونُ مُضْغَةً مِثْلَ ذَلِكَ، ثُمَّ يُرْسَلُ إلَيْهِ الْمَلَكُ فَيَنْفُخُ فِيهِ الرُّوحَ، وَيُؤْمَرُ بِأَرْبَعِ كَلِمَاتٍ: بِكَتْبِ رِزْقِهِ، وَأَجَلِهِ، وَعَمَلِهِ، وَشَقِيٍّ أَمْ سَعِيدٍ؛ فَوَاَللَّهِ الَّذِي لَا إلَهَ غَيْرُهُ إنَّ أَحَدَكُمْ لَيَعْمَلُ بِعَمَلِ أَهْلِ الْجَنَّةِ حَتَّى مَا يَكُونُ بَيْنَهُ وَبَيْنَهَا إلَّا ذِرَاعٌ فَيَسْبِقُ عَلَيْهِ الْكِتَابُ فَيَعْمَلُ بِعَمَلِ أَهْلِ النَّارِ فَيَدْخُلُهَا. وَإِنَّ أَحَدَكُمْ لَيَعْمَلُ بِعَمَلِ أَهْلِ النَّارِ حَتَّى مَا يَكُونُ بَيْنَهُ وَبَيْنَهَا إلَّا ذِرَاعٌ فَيَسْبِقُ عَلَيْهِ الْكِتَابُ فَيَعْمَلُ بِعَمَلِ أَهْلِ الْجَنَّةِ فَيَدْخُلُهَا”.

[رَوَاهُ الْبُخَارِيُّ]

، [وَمُسْلِمٌ]

ALHADITHUR RABI’U (4)
An Abi Abdurrahmani Abdullahi ibn Mas’udin (RA) Kala: Haddathana Rasulullahi (SAW), wahuwas saadiKul masduuKu “Inna ahadakum yujma’u khalKuhuu fii batni ummihii arba’ina yauman nutfatan, thumma yakuunu alaKatan mithla dhaalika, thumma yakuunu mudgatan mithlu dhaalika, thumma yursalu ilaihil malaku fayanfakhu fihir ruuha wa yuumaru bi’arba’i kalimaatin bi katbi rizKihii, wa ajalihii, wa amalihi, wa shaKiyyun au sa’idun.

Fa wallaahil ladhii La’ilaha gairuhuu in ahadakum laya’amalu bi amali ahlil jannati hatta maa yakuunu bainahuu wa bainahaa illaa dhiraa’un fayasbiKu alaihil kitaabu faya’amalu bi amali ahlin naari fa yadkhuluha, wa inna ahadakum laya’amalu bi amali ahlinnaari hatta ma yakuunu bainahuu wa bainahaa illa dhira’un fayasbiK ualaihil kitaabu faya’amalu bi amali ahlil jannati fayadkhuluhaa”.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 2

Rawahul Bukhari wa Muslimu.

HADISI NA HUDU (4)
An rawaito daga Abdurrahman Abdullahi dan Mas’udu (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) mai gaskiya abin gasgatawa, ya ba mu labari, ya ce: “HaKiKa ana tattara halittar dayanku (wato mutum) a cikin mahaifiyarsa, kwana arba’in yana maniyyi sannan ya zama gudan jini, misalin haka, (wato kwana (40) sannan ya zama tsoka kamar haka, kwana arba’in, sannan a aiko Mala’ika domin ya busa masa rai, sannan kuma a umarce shi da kalmomi hudu, zai rubuta arziKinsa da ajalinsa, da kuma ko tababbe ne shi, ko mai rabo.

Na rantse da Allah, wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi, haKiKa dayanku zai yi aiki irin aikin ‘yan aljanna, har sai ya kasan ce tsakanin sa da tsakanin ta saura zira’i daya, sai littafi, ya rigaya a gare shi sai yayi aiki irin na ‘yan wuta sai ya shige ta.

Haka kuma haKiKa dayanku zai yi aiki irin aikin ‘yan wuta, har sai ya kasance tsakaninsa da tsakaninta saura zira’i daya, sai littafi ya rigaya a gare shi sai ya yi aiki irin aikin ‘yan aljanna, sai ya shige ta! Bukhari da Muslimu ne suka rawaito shi.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: