Hadisi Na Daya (1) -Arbauna Hadis

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Muna tafe da hadis na daya a cikin littafin arba’una hadis.

Hadis din yana magana akan niyya,

Talla

عَنْ أَمِيرِ الْمُؤْمِنِينَ أَبِي حَفْصٍ عُمَرَ بْنِ الْخَطَّابِ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم يَقُولُ: ” إنَّمَا الْأَعْمَالُ بِالنِّيَّاتِ، وَإِنَّمَا لِكُلِّ امْرِئٍ مَا نَوَى، فَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُهُ إلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ فَهِجْرَتُهُ إلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ، وَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُهُ لِدُنْيَا يُصِيبُهَا أَوْ امْرَأَةٍ يَنْكِحُهَا فَهِجْرَتُهُ إلَى مَا هَاجَرَ إلَيْهِ”.

رَوَاهُ إِمَامَا الْمُحَدِّثِينَ أَبُو عَبْدِ اللهِ مُحَمَّدُ بنُ إِسْمَاعِيل بن إِبْرَاهِيم بن الْمُغِيرَة بن بَرْدِزبَه الْبُخَارِيُّ الْجُعْفِيُّ [رقم:1]، وَأَبُو الْحُسَيْنِ مُسْلِمٌ بنُ الْحَجَّاج بن مُسْلِم الْقُشَيْرِيُّ النَّيْسَابُورِيُّ [رقم:1907] رَضِيَ اللهُ عَنْهُمَا فِي “صَحِيحَيْهِمَا” اللذَينِ هُمَا أَصَحُّ الْكُتُبِ الْمُصَنَّفَةِ

ALHADITHUL AUWALU (1)
An amiril mu’iminina Abi Hafsin Umara Ibn Khaddabi, (RA) Kala: Sami’itu Rasulallahi (SAW) yaKulu: “Innamal a’amalu binniyati wa’innama li kulli imiri’in ma nawa, faman kanat hijratuhu ilallahi wa Rasulihi, fahijratuhu ilallahi wa Rasulihi waman kanat hijiratuhu lidunya yusibuha aw imra’atin yankihuha fa hijiratuhu ila ma hajara ilaihi”.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 2

Rawahu Imamal muhaddithina Abu Abdullahi Muhammadu Ibn Isma’ila, Ibn Ibrahima, Ibn Mugirata, Ibn Bardizbah Al-bukhariyyu, wa Abu Hussaini, Muslimu Ibn Hajjaji Ibn Muslimin Al-Kushairiyyu Annaisaburiyyu fii sahihaihima alladhaini huma asahhul kutubi almusannafati.

HADISI NA DAYA (1)
An rawaito daga Sarkin Mu’uminai Abi Hafs, Umar dan Khattab, (RA) ya ce: Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Dukkanin ayyuka ba sa yiwuwa sai da niyya, kuma kowane mutum akwai abin da ya niwaita ya tabbata gare shi.

Wanda hijirar sa ta kasance saboda Allah da Manzon sa to, hijirarsa ta tabbata izuwa ga Allah da Manzonsa, wanda kuma hijirarsa ta kasance don duniya, ko kuma wata mace don ya aureta, to haKiKa hijirarsa ta tabbata izuwa abin da ya yi hijirar izuwa gare shi”.

Shugabannin masu ruwaito hadisai ne suka rawaito shi, su ne Abu Abdullahi Muhammadu dan Isma’ila, dan Ibrahima, dan Mugirata, dan Bardizba, Al-Bukhari, da kuma Abu Husaini Muslimu dan Hajjaju da Muslim Al-Kushairi, Al-Nisaburi a cikin ingantattun nan guda biyu wadanda su ne mafi ingancin littatafin ababar tsarawa.

Daga Abubakar Salihu Kabara

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: