Hadisi Na Biyu (2) -Arba`una Hadis

0 940

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Muna tafe da hadisi na biyu cikin littafin arba’una hadis wanda yake bayani akan musulunci, imani,kyautatawa, alamomin, tashin alqiyama.

عَنْ عُمَرَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ أَيْضًا قَالَ: ” بَيْنَمَا نَحْنُ جُلُوسٌ عِنْدَ رَسُولِ اللَّهِ صلى الله عليه و سلم ذَاتَ يَوْمٍ، إذْ طَلَعَ عَلَيْنَا رَجُلٌ شَدِيدُ بَيَاضِ الثِّيَابِ، شَدِيدُ سَوَادِ الشَّعْرِ، لَا يُرَى عَلَيْهِ أَثَرُ السَّفَرِ، وَلَا يَعْرِفُهُ مِنَّا أَحَدٌ. حَتَّى جَلَسَ إلَى النَّبِيِّ صلى الله عليه و سلم . فَأَسْنَدَ رُكْبَتَيْهِ إلَى رُكْبَتَيْهِ، وَوَضَعَ كَفَّيْهِ عَلَى فَخِذَيْهِ،

وَقَالَ: يَا مُحَمَّدُ أَخْبِرْنِي عَنْ الْإِسْلَامِ.

فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه و سلم الْإِسْلَامُ أَنْ تَشْهَدَ أَنْ لَا إلَهَ إلَّا اللَّهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ، وَتُقِيمَ الصَّلَاةَ، وَتُؤْتِيَ الزَّكَاةَ، وَتَصُومَ رَمَضَانَ، وَتَحُجَّ الْبَيْتَ إنْ اسْتَطَعْت إلَيْهِ سَبِيلًا.

قَالَ: صَدَقْت . فَعَجِبْنَا لَهُ يَسْأَلُهُ وَيُصَدِّقُهُ!

قَالَ: فَأَخْبِرْنِي عَنْ الْإِيمَانِ.

قَالَ: أَنْ تُؤْمِنَ بِاَللَّهِ وَمَلَائِكَتِهِ وَكُتُبِهِ وَرُسُلِهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ، وَتُؤْمِنَ بِالْقَدَرِ خَيْرِهِ وَشَرِّهِ.

قَالَ: صَدَقْت. قَالَ: فَأَخْبِرْنِي عَنْ الْإِحْسَانِ.

قَالَ: أَنْ تَعْبُدَ اللَّهَ كَأَنَّك تَرَاهُ، فَإِنْ لَمْ تَكُنْ تَرَاهُ فَإِنَّهُ يَرَاك.

قَالَ: فَأَخْبِرْنِي عَنْ السَّاعَةِ. قَالَ: مَا الْمَسْئُولُ عَنْهَا بِأَعْلَمَ مِنْ السَّائِلِ.

قَالَ: فَأَخْبِرْنِي عَنْ أَمَارَاتِهَا؟ قَالَ: أَنْ تَلِدَ الْأَمَةُ رَبَّتَهَا، وَأَنْ تَرَى الْحُفَاةَ الْعُرَاةَ الْعَالَةَ رِعَاءَ الشَّاءِ يَتَطَاوَلُونَ فِي الْبُنْيَانِ. ثُمَّ انْطَلَقَ، فَلَبِثْتُ مَلِيًّا،

ثُمَّ قَالَ: يَا عُمَرُ أَتَدْرِي مَنْ السَّائِلُ؟.

‫‬قُلْتُ: اللَّهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ.

قَالَ: فَإِنَّهُ جِبْرِيلُ أَتَاكُمْ يُعَلِّمُكُمْ دِينَكُمْ “. [رَوَاهُ مُسْلِمٌ]

ALHADITHUT THANI (2)
An Umara (RA) aidan Kala: bainama nahnu julusun inda Rasulillahi (SAW) dhata yaumin idh tala’a alaina rajulun shadisu bayadit thiyabi shadidu sawadis sha’ari, la yura alaihi atharus safari wala ya’arifuhu minna ahadun hatta jalasa ilan Nabiyyi (SAW) fa’asnada rukbataihi ila rukbataihi, wawada’a kaffaihi ala fakhidhaihi.

WaKala: Ya Muhammadu! Akhbirnii anil Islami, faKala Rasulillahi (SAW):

“Al-Islamu an tashhada an La’ilaha ilallahu, wa anna Muhammadan Rasulullahi, wa tuKimus salata, wa tu’utiyaz zakata, wa tasuma Ramadana wa tahujjal baita inista-ta’ata ilaihi sabilan”.

Kala sadaKta fa’ajibna lahu yas’aluhu wayusaddiKuhu!

Kala fa’akhbirnii anil imani Kala:

“An tu’umina billahi, wa mala’ikatihi, wa kutubihi, wa Rasulihi, wal yaumil akhiri wa tu’imina bil Kadri khairihi wa sharrihii”.

Kala sadaKta.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 2

Kala: fa’akhbirnii anil ihsani Kala:

“An ta’abdullaha ka’annaka taraahu, fa’in lam takun taraahu fa’innahuu yaraaka”.

Kala: fa’akhbirnii anissa’ati Kala:

“Malmas’uulu anha bi a’alama minassa’ili”.

Kala: fa’akhbirnii an amaaraatihaa. Kala:

“An talidal amatu rabbataha, wa an taral hufata al-urata al’aalata ri’a’assha’i yatataawaluuna fil bunyaani!.

Thumman talaKa falabithtu maliyyan thumma Kala:

“Ya Umaru atadrii manis sa’ilu?”

Kultu: Allahu wa Rasuuluhuu a’alamu.

Kala: “Fa’innahuu Jibrilu ataakum yu’allimukum dinakum”. Rawahu Muslimun.

HADISI NA BIYU (2)
An rawaito daga Sayyadina Umar (RA) kuma, ya ce: tsakananinmu muna zaune a wajen Manzon Allah (SAW) wata rana sai wani mutum ya bullo a gare mu, wani mai tsananin farin tufafi, mai tsananin baKin gashi, babu wanda yake ganin gurbin tafiyar sa, kuma babu wanda ya san shi daga cikinmu har ya zo ya zauna kusa da Manzon Allah (SAW), sai ya jingina gwiwowinsa izuwa gwiwowin Manzon Allah, kuma ya dora tafukansa a bisa tafukan Manzon Allah (SAW),

Sannan sai ya ce: (Ya Muhammadu ba ni labari a bisa Musulunci, sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Musulunci shi ne ka shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi (SAW) Manzon sa ne. ka tsai da sallah, kuma ka ba da Zakka. Ka yi azumin watan Ramadana. Ka ziyarci dakin Allah Mai Girma idan ka sami ikon zuwa gare shi).

Sai ya ce: ka yi gaskiya, sai muka yi mamakinsa yana tambayarsa kuma yana gasgata shi.

Sannan sai ya ce: To, ba ni labari a bisa Imani. “Sai Annabi ya ce: “Ka yi imani da Allah, da Mala’ikunsa, da littattafansa da Manzanninsa, da ranar lahira, kuma ka yi imani da Kaddara, (wato alkhairinsa da kuma kishiyar sa).

Sai ya ce: To, ba ni labari a kan kyautatawa: sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Shi dai ihsani (Kyautarawa) shi ne ka bautawa Allah kai ka ce kana ganinSa, idan ka kasance ba ka ganinSa to shi yana ganinka”.

Sai ya ce: Ba ni labari a kan tashin alKiyama! Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: Wanda ake tambayar baifi wanda yake tambayar sani ba.

Sai ya ce: ba ni labarin alamominta (tashin Alkiyama). Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: (Alamominta) idan baiwa ta haifi uwangijiyarta. Kuma zakaga masu tafiya ba takalmi matsiraita talakawa masu kiwon dabbobi, suna tsawaitawa cikin gine-gine.

Sai mai tambayar ya tafi Muka zauna zamani mai tsawo.

Sannan sai ya ce: Ya Umaru ko ka san wannan mai tambayar?

Sai na ce: Allah da Manzonsa ne suka sani, sai ya ce: to, wannan dai Jibrilu ne ya zo muku domin sanar da ku addininku. Muslimu ne ya rawaito shi.

Daga Abubakar Salihu Kabara

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: