Labarai

HADARIN JIRGIN SU JANAR ATTAHIRU: Boko Haram Da Shi’a Sun Ji Kunya

Daga Sister Fatima Aliyu
Lokacin da labarin faɗuwar jirgin saman shugaban dakarun sojin Nijeriya Janar Ibrahim Attahiru ta zo mini na samu damuwa da kidimewa akai, bisa ga la’akari da irin gagarumin rashin da Nijeriya ta yi.

Amma a hannu guda bayan nazari da nayi sai na fahimci akwai aya a rasuwar wannan babban gwarzo jarumin Janar Ibrahim Attahiru shugaban dakarun sojin ƙasa.

Da farko inda a ce hatsarin jirgin ya faru ne a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan, to da babu shakka Ƙungiyar Boko Haram za ta fito ta yi ikirarin cewa ita ta harbo jirgin, wanda kuma dole a yarda da hakan babu musu, kuma tabbas da barazanar Boko Haram ta ƙara yin sama da faruwar hakan.

Hakazalika da a ce tsohon Shugaban Dakarun Soji Janar Buratai ne ya yi wannan hadari akan hanyar shi ta zuwa Zariya, to da babu shakka da ‘yan Shi’a sun cika ƙasa da ihu da hayaniyar cewa mu’ujizar Zakzaky ta kashe shi.

Amma da yake Allah gwani mai hikima ne sai ya kunyartar da dukkanin kungiyoyin biyu na Boko Haram da Shi’a! Alhamdulilah Allah mun gode maka!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: