Labarai

Hada-hadar Cinikin Makamai Ya Yi Sama – Binciken Stockholms

Bincike ya nuna a cikin wani sabon rahoto da ke bayyana cewa masu sayar da makamai a duniya suna ciniki sosai a lokutan nan, wanda ba a taba samun hakan ba tun bayan yakin Duniya na 2 (world war II).
Daga shekarar 2012 zuwa bara, cinikin siyar da makamai ya tashi da kashi 8 cikin 100, idan aka kwatanta da shekaru 5 da suka gabata, sakamakon binciken da kwarraru daga cibiyar Stockholms Internation Peace Research su ka fitar.
Kasashen da suka fi sayen makamai sune kasashen da su ke yankin Golf da kuma gabas ta tsakiya, inda kasar Saudiyya ta fi kowacce sayen makamai sai kuma kasar India.
Daga karshe, rahoton ya nuna cewa kasashen Amurka, da Rasha, da China, da Faransa da kuma Jamus ke da mallakar kashi 75 cikin 100 na makaman duniya.