Wasanni

Haaland Ba Na Sayarwa Ba Ne, Cewar Dortmund

Shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund take kasar Jamus, Michael Zorc, ya bayyana cewa dan wasan kungiyar Erling Braut Haaland bana sayarwa bane akan kowanne farashi.

Tun a satin daya wuce ne Dortmund dake kasar Jamus ta bayyana cewa ba za ta sayar da dan wasanta Erling Braut Haaland ba a bana, bayan da Chelsea ke son daukar dan kwallon kuma har ta kai tayin kudi.

Sai dai rahotanni sun ruwaito cewa Chelsea ba ta taya dan kwallon ba, wanda zai cika shekara 21 ranar 21 ga watan Yuli duk da cewa wasu daga cikin jaridun kasar Jamus sun bayyana cewa anyi tayin kudin kuma nan take akayi fatali da tayin.

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Thomas Tuchel ya bayyana cewa yana son salon buga wasa dan wasa Haaland dan kasar Norway wanda ya ci kwallaye 20 a wasanni 16 daya buga a gasar cin kofin zakarun turai na Champions League a Red Bull Salzburg da kuma Borussia Dortmund sannan shima kocin Manchester City, Pep Guardiola na bibiyar dan wasan.

Shima kociyan Manchester City Pep Guardiola dan kasar Sifaniya, yana neman mai cin kwallaye bayan da Sergio Aguero ya koma Barcelona, wanda yarjejeniyarsa ta kare a kungiyar a bana sannan ana kuma alakanta Manchester City da cewar tana son yin zawarcin dan wasan Ingila, Harry Kane, wanda ake cewar zai bar Tottenham a bana.

Kungiyar wadda zata buga kofin zakarun turai a shekara mai zuwa ta ce ba za ta sayar da Haaland ba, kuma zai ci gaba da yi mata wasanni a kakar da za a fara cikin watan Agusta mai zuwa.

A cewar Zorc “Sancho kadai muka amince mu sayar a bana amma sauran ‘yan wasan mu za su ci gaba da buga mana wasa har zuwa kakar wasa mai zuwa kafin muyi tunanin sayar dasu ga kungiyar da take bukata”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: