Labarai

Haɗin gwiwa da jami’an Kasar Chadi da Kamaru da Nijar na iya kawo karshen ta’addancin Boko haram, Cewar Gwamna Zulum

Daga El-farouq jakada

Gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Umaru Zulum, yayi kira kan canza jami’ai da fatan zai kawo canji matuƙa ga matsalar tsaro daya addabi yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Sannan ya jaddada yin haɗin gwiwa da jami’an Kasar Chadi da Kamaru da Nijar zai kara tallafawa sosai wajen ganin an kawo karshen ta’addanci yan kungiyar Boko Haram a Afrika bakidaya.

Ya bayyana Hakane a zantawar da yayi da Manyan hafsoshin da gwamnatin tarayya ta canza wato (Chief of Defence, Major General Lucky Irabor, Sai Major General Ibrahim Attahiru Wato Chief of Army Staff, Sannan Naval staff Rear Admiral Zubairu Gambo da kuma Air Staff Air vice Marshall Oladayo Amao).

Wannan tattaunawa ta gudana a jihar ta Borno dake tarayyar Najeriya, inda suka tattauna sosai don ganin an kawo karshen ta’addanci a faɗin Kasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: