Gwamnonin Arewa Za Su Yi Wa Ganduje Da Sarki Sanusi Sulhu — Gwamna Shettima


1 209

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Gwamnna Borno wanda kuma shi ne shugaban kungiyar Gwamnonin Arewaa mai barin gado Kashim Shettima a ranar Juma’a ya bayyana cewa shi da wasu Gwamnonin Arewa na kokarin sulhunta sa toka sa katsin da ke faruwa tsakanin Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II.

Gwamna Kashim Shettima wanda ya yi magana da manema labarai a lokacin taron Gwamnonin Arewa da aka gudanar a Kaduna, ya ce, duk da dai gwamnonin ba suda hurumin shiga cikin matsalolin wasu jihohin, yace suna da sha’awa ko fatan ganin an kawo karshen  fito na fiton da ke faruwa a Jihar Kano musamman yadda al’amarin ke shafar rayuwar al’umma.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 636

- Advertisement -

Gwamna Shattima yace Gwamna Ganduje da mai martaba Sarkin Kano sun yi wasu abubuwa masu muhimmanci  ga al’ummar Jihar Borno musamma ma ni kai na, domin Gwamnan Ganduje ne ya samar da tallafin Karatu ga marayu 200 tun daga matakin firamare har zuwa Jami’a  wadanda aka kashe iyayensu a rikicin Boko Haram. Ya ce an samarwa wadannan yara wurin kwana, abinci da kuma tabbatar da basu ingantaccen ilimi a Jihar Kano karkashin tsarin kulawa ta musamman da Gwamnan ya amince dashi.

Gwamna Shettima ya ci gaba da cewa a daya bangaren kuma Mai Martaba Sarkin Kano  shi ne ya zama mai shiga tsakaninmu da Alhaji Aiko Dangote a shekara 2016, sarkin ya je Jihar Borno domin ganin halin da ake ciki,  wanda hakan tasa ya yi Magana da Dangote, wanda hakan tasa Dangote zuwa Maiduguri har sau uku.

Dangote ne ya bayar da gudunmawar data zarta duk wata gudunmawar da kungiyoyi da daidaikun mutane suka bayar,  haka kuma  ba zan manta abinda Sarkin Kano ya yi mana ba na hada mu da gwmanan Babban Bankin Kasa, Sarkin ne ya kawo Gwamnan Babban Bankin  Jihar Borno a cikin shekara ta 2013 Sarkin na Kano ya taimaka kwarai da gaske wajen wayar da kai acikin gida da kuma kasashen waje kan halin da Jihar Borno ta tsinci kanta a ciki,  don haka ba zan manta irin tausayawar  da sarkin da kuma Gwamna Ganduje suka nuna ba, wanda hakan ce tasa  na ke kokarin bayar da gudunmawa wajen samar da daidaito tsakanin mutanen biyu. Gwamna Shettima yace kamar yadda aka sani mu gwamnoni muna da wani tsari na cewa bama katsalandan cikin harkokin wasu johohin, sai dai kawai muna yin duk mai yiwuwa ta karkashin kasa domin sulhuntawa. Ba zan iya cewa ga yadda Gwamna Ganduje zai jagorantar Jihar Kano ba, amma dai zamu iya samar da wata gada  tare da taimakon ubangiji domin ganin Gwamna Ganduje da Sarkin Kano sun koma tare  kamar yadda suke a baya, a cewar Shettima.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.