Daga Hausa Times: Wasu daga cikin manyan yan siyasar kasarnan da suka hada da ministoci da Gwamnoni mabiya akidar ‘Buhariyya’ suna bakin kokarinsu domin tabbatar da shugaba Muhammadu Buhari ya sake tsayawa takara a 2019.
Bayanin hakan ya fito ne daga jigo a kungiyar tasu da sukayiwa suna akidar “Buhariyya zalla”, Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai a hirarsa da manema labarai yau a Aso Villa jim kadan da kammala ganawarsa da shugaba Buhari.
Yace dukkanunsu sun dukufa tsara fasalin yadda shugaban zai zarce a 2019 domin karasa ayyukan da ya fara na farfado da Nigeria.
El-Rufai ya kuma karyata batun da ake yadawa cewa yana da muradin takarar shugabancin Nigeria a 2019. Yace shi ko fitowa takarar Gwamna baya nema a yanzu domin shi da gungun magoya bayan akidar Buhari basu yanke komi ba sai abunda shugaba Buharin ya umurcesu.
Gwamnan yace ” a cikinmu Gwamnoni da ministoci akwai wadanda muka ware kanmu, wato “yan akidar Buhariyya” dukkanmu babu mai wani buri a yanzu da ya wufe kokarin gani da addu’ar Allah ya karawa Baba Buhari lafiya da kuzari domin ya zarce a 2019 kuma aikin da mukeyi kenan ba dare ba rana”
Add Comment