Labarai

Gwamnatin Tarayya Zata Haramta Ayyukan Ƙungiyar Afenifere Da Ta Yiwa Annabi (S.A.W) Ɓatanci

Kamar yanda dai aka haramta ayyukan ƙungiyar IPOB, Gwamnatin tarayya na shirin haramta ayyukan ƙungiyar Yarabawa ta Afenifere.

Kungiyar Yarabawa ta Afenifere, ita ce ta yiwa Annabi Muhammad (S.A.W) ɓatanci wanda Sahara Reporters ta wallafa kuma ya jawo musu tofin Allah tsine.

Babban lauyan gwamnati kuma ministan shari’a, Abubakar Malami ya bayyana aniyar gwamnati na son haramta ayyukan ƙungiyar Afenifere.

Yace Gwamnati na duba yiyuwar hakan ne dan tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya a Najeriya. Za’a haramta ayyukan Afenifere ne, musamman saboda yanda take da alaƙa da mai fafutukar kafa ƙasar Oduduwa, Sunday Igboho.

Kakakin Malami, Umar Gwandu ne ya bayyana haka a ganawarsa da manema labarai, yace kuma ba gaskiya ba ne iƙirarin da ake cewa, wai gwamnati bata hukunta ƴan ta’adda.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: