Labarai

Gwamnatin Tarayya Zata Bada Bashin Gidaje

Cikin wannan makon ne gwamnatin shugaba Buhari zata gabatar da wani shiri na musamman ga ‘yan kasa, shirin wanda aka yi ma suna da “National Social Housing Program”, ko NSHP a takaice, wato “Shirin samar da gidaje ga al-umma na ‘kasa”, wannan yana cikin shirin shugaban kasar na “Economic And Sustainability Plan”, zai bada dama ga ‘yan kasa su mallaki gida mai kyau mai inganci a duk inda suke a fadin Nigeria akan kudi mai sauki ta hannun gwamnatin tarayya.
.
Wannan shirin zai baka dama gwamnati ta gina maka gida irin wanda kake so, a duk inda kake so matukan acikin Nigeria ne.
Daga na Naira miliyan biyu 2,000,000 zuwa na Naira miliyan uku da rabi, 3,500,000.
Wanda yanzu shugaba Buhari ya amince da fitar da kudaden dan fara wannan aiki dan amfanar jama’an Nigeria.
.
Wanda zaka ka rinka biya kadan kadan kadan zuwa wasu shekaru.
Yanzu haka an kusa budewa, kuma online zaka cika, ba wani Ofis zaka je ba, amma yanzu haka zaka iya hawa website din ka cike “Interest Form” wato Form din nuna kana bukatan gida.
A wannan site din https://nshp.gov.ng
.
Tsarin gidajen an kasa su kasu kashi uku:
1.
Two Rooms (1 Bedroom House) a Naira ₦2,000,000.
2.
Three Rooms (2 Bedroom House) a Naira ₦2,750,000.
3.
Four Rooms (3 Bedroom House) Naira ₦3,500,000.
Idan kana bukata zaka zaba wanda kake so, gwamnatin zasu tun-tube ka, suje ka nuna musu fili, su tabbatar da mallakar ka ne, sannan su gina maka.
.
‘Ka’idojin da sai ka cika su kafin a gina maka:
1. Dole sai ‘dan Nigeriya.
2. Dole sai ka kai shekaru 18 ko sama da haka.
3. Any national means of identification.
National I.D card, Driving Lc, Voters card, ko International Passport.
.
Wannan shirin gina gidajen zai samar da aikin yi ga matasa miliyan 1 da dubu dari takwas.
Daga masu Blocks, gini, yashi, dutsi, Inter locks, kafintoci, masu aikin wiring na ruwa, masu aikin wutar lantarki, masu Fenti da sauran su, mutane da yawa zasu samu aikin yi na samun kudi idan an fara wadannan gine ginen a fadin kasar nan.
.
Gwamnatin bata ware wani wurin da za’a gina gidajen ba, sai dai duk wurin da ka so kawai, ko a birni ko a kauye za’a je har wurin a gina maka, daga baya ka biya.
Sai dai kayi kokari ka tabbatar da filin naka ne.
Ka mallaki takardun filin, Kar azo kace musu ai Baban ku ne ya mutu ya bar maka, a’a, suna son abu a rubuce a zahiri.

Haarun

Haruna Lawan Usman is a certified Animal Health and Production Technologist, with more than 4 years experience in Animal Health and Production Technology.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: