A yunkurin ta na kawo karshen karancin jami’an tsaro da ake fuskanta a kasar, gwamnatin tarayya ta baiwa rundunar ‘yansanda damar daukar sabbin jami’ai har guda 10,000 a duk shekara.
Babban Sifeton ‘yan sanda, Ibrahim Idris shi ya tabbatar da haka yayin da ya ke jagorantar wani taro na manyan jami’an ‘yan sanda a birnin tarayya Abuja.
Idris ya ce wannan mataki ya zama wajibi idan har za a kawo karshen aikata miyagun laifuka a Nijeriya.
Ya ce a yanzu haka akwai dan sanda daya ga kowanne mutum 400 a Nijeriya, kuma wannan mataki zai taimaka wajen rage wannan alkaluma.
Babban sifeton ‘yan sandan ya kuma yi kira ga majalisa da ta gaggauta sanya hannu a kan kudirin da aka gabatar mata na kara adadin kudaden da ake warewa hukumar ‘yan sandan kasar.
Add Comment