Labarai

Gwamnatin Tarayya Tayi Amai Ta Lashe Akan Komawa Makarantu

– FG ta bayyana cewa bata amince da masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi ba kan komawa makarantu a ranar 18 ga watan Janairu

– Wasu makarantu a fadin Najeriya sun koma harkokin karatu a ranar Litinin, 18 ga watan Janairu

– Sai dai kuma, ministan ilimi Adamu Adamu, ya bayyana cewa za a sake duba batun komawa makarantun

Gwamnatin tarayya a ranar litinin, ta ce tana adawa da batun komawa makarantu a ranar 18 ga watan Janairu.

A wajen taron tattaunawa na kwamitin fadar shugaban kasa kan korona, ministan ilimi, Adamu Adamu, ya ce gwamnatin tarayyar bata amince da matsayar jihohi kan ranar komawa makaranta ba.

Adamu, wanda ya bayyana cewa PTF za ta lura da yanayin korona a kulla yaumin, ya ce ana iya sake duba batun ranar komawa makarantu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

COVID-19: FG tayi amai ta lashe, ta ce bata yarda da bude makarantu a ranar 18 ga Janairu ba Hoto: @DigiCommsNG
Source: Twitter.

“Mun zauna, mun duba alkaluman sannan muka yanke shawarar cewa kada a bude makarantu.

“Abun bakin ciki, ya zama dole mu bayyana wannan saboda ya kamata ace ya zama hukuncin bai daya, amma ya zama dole ku fahimci cewa maganar makarantu ake yi, gwamnatin tarayya na da kimanin makarantu 100 ne kawai cikin dubban makarantu.

“Makarantun na karkashin ikon jihohi ne kuma yayinda PTF ta ce hada kai wajen cewa kada a bude makarantu, jihohi sun hade cewa a bude makarantu.

“Don haka, ya zama dole mu sasanta sannan a matsayinmu na PTF za mu lura da abubuwan da ke faruwa a kulla yaumin. Ana iya sake duba lamarin,” in ji Adamu.

 

Haarun

Haruna Lawan Usman is a certified Animal Health and Production Technologist, with more than 4 years experience in Animal Health and Production Technology.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: