Gwamnatin tarayya ta Fara ƙudirin kirkiro da matsakaitun masana’antu a Kananan Hukumomin 774 dake Najeriya

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

… Gwamnatin tace tanasa ran kashe kuɗi naira tiriliyan N1 ne domin cimma wannan ƙudiri.

Daga El farouq jakada

Ministan Ayyuka na Musamman, Sanata George Akume ne ya bayyana hakan yayin ganawarsu da Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Ayyuka na Musamman. Inda ya ce irin wannan masana’anta ta cikin gida za ta maida hankali ne wajen samar da kayayyakin masarufi don amfanin al’ummar yankin da aka kafa masana’antar a cikinta.

Da yake amsa tambayoyin mambobin kwamitin, Ministan ya ce yanzu haka suna kan tattaunawa tare da Shugaban Ƙasa kan batun. Tare da cewa idan Shugaban Ƙasa da Majalisar Zartarwa suka amince da batun, ma’aikatarsa za ta soma aikin gina masana’antu a cikin Yuni mai zuwa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 732

Haka nan, ya ce akwai wani shiri na daban da ɓangare mai zaman kansa ya yi inda zai kashe kuɗi tiriliyan N19 ga shirin samar da masana’antun a sassan ƙasa a tsakanin shekaru goma, baya ga Naira tiriliyan guda da Gwamnatin Tarayya ta shirya kashewa.

Ministan ya bayyana cewa Naira tiriliyan guda da gwamnati ke sa ran kashewa za ta samo kuɗin ne daga ƙoƙarin ɓangare mai zaman kansa wanda za ta biya kuɗin ruwa na kashi 2 wanda hakan ne ma ya kwaɗaita wa ‘yan kasuwar yanke shawarar shigowa don a yi aikin tare.

A cewar Ministan, “Da muka ce masana’antar cikin gida, muna nufin masana’antu irin waɗanda ke da ƙarfin samar da abubuwa irin su; kayan shayi da lemon kwalba da makamantansu, amma ba samar da siminti ko motoci ba.”

Tun farko sa’ilin da yake jawabi, Shugaban kwamitin, Sanata Abubakar A. Yusuf (APC dagaTaraba ta Tsakiya), ya buƙaci ƙarin haske kan ko Naira tiriliyan guda da gwamnati tace zata kashe, daga aljihun gwamnati kuɗin zai fito ko kuwa a jikin ‘yan kasuwa.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: