Gwamnatin tarraya Nijeriya ta fitar da kimanin naira 844,360,550 don ciyar da sama da daliban makarantun firamari miliyan daya a jihohi guda bakwai na kasar nan.
Mista Laolu Akanda mashawarcin mataimakin shugaban kasa ta bangaren watsa labarai ya shaida wa yan jaridu a ranar Litinin yayin da yake tsatsage bayani dangane da shirin ciyar da dalibai na Gwamnatin shugaba Buhari
Ya zayyana jihohin da zasu amfana yan rukunin farko a matsayin Anambra, Ebonyi, Enugu, Oyo, Osun, Ogun da Zamfara.
Add Comment