Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Gina Sabuwar Jami’ar Fasaha

Daga Engr Magaji Abdullahi Mallammadori
Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, a madadin Gwamnati da al’umar Jihar Jigawa masu daraja, yana miƙa matuƙar godiya maras misaltuwa ga Maigirma Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, bisa amincewa da sahalewar sa na samar da sabuwar Jami’ar Fasaha na Tarayya a garin Babura na Jihar Jigawa, a ɗaya daga cikin sabbin jami’o’i huɗu da ya amince a kafa su.

Gwamna Badaru ya kuma ƙara jaddada godiyar sa maras misaltuwa ga Maigirma Shugaban Ƙasan bisa ƙara amincewa da yayi na samar da zunzurutun kuɗaɗe har Naira Biliyan Huɗu domin fara gudanar da harkokin sabuwar Jami’ar Fasaha ta Tarayya na garin Babura, wanda ya bayyana cewa wannan tagomashi da gwaggwaɓan kulawa, ya nuna cewa Maigirma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, bayan cikakkiyar soyayya da ƙauna da yake nunawa Gwamnati da al’umar Jihar Jigawa, ya kuma ƙara tabbatar da irin kishin da yake da shi na samar da tabbataccen cigaba mai ɗorewa a fannin ilimi.

Idan zamu iya tunawa, Gwamnatin Tarayya a kwanakin bayan nan ta sanar da ƙudurinta na samar da sabbin jami’o’i domin magance ƙarancin ma’aikata da Ƙasar ke fama da shi a ɓangarori da fannoni na fasaha, kiwon lafiya da abinci masu gina jiki.

Sabbin jami’o’in da aka ƙirƙira za’a samar da su a Jihohin Jigawa, Akwa Ibom, Osun da Bauchi, a yayin da za’a ɗaga darajojin guda huɗu (Jami’o’in Fasaha na Tarayya) da ake da su a baya.

Gwamna Badaru wanda yake ciki da farin ciki a yayin da ya karɓi Takardar da ya samu daga Ministan Ilimi na Tarayya Malam Adamu Adamu akan kafa sabuwar Jami’ar, ya kuma godewa Ministan na Ilimi da duk sauran mutanen da suka yi aiki tuƙuru wajen tabbatar da cewa Maigirma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da kuma ganin an kawo Jami’ar Tarayya na Fasahar garin Babura.

Gwamna Badaru yace samar da sabuwar Jami’ar a garin Babura abu ne da al’umar yankin Jigawa ta Arewa maso Yamma suka jima na burin suga an samu Jami’a ta Gwamnati, wanda hakan ya tabbata a lokacin mulkin Shugaba Buhari, kasancewar sauran yankunan biyu sun rabauta da Jami’a a Dutse da kuma garin Kafin Hausa.

Har wa yau, Gwamna Badaru ya kuma jinjina tare da miƙa godiyar sa ga Santocin Jihar Jigawa da dukkanin ƴan Majalisun Tarayya na Jihar da suka dinga faɗi tashi da kai kawo zuwa Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya domin ganin hakan ta tabbata.

Maigirma Gwamnan ya tabbatarwa da Shugaba Buhari haɗin kan al’umar Ƙaramar Hukumar Babura na marawa Jami’ar, tare da Hukumar Gudanarwar ta, Ma’aikata da Ɗaliban Jami’ar ta kowanne ɓangare da zaran Jami’ar ta fara aiki, inda ya kuma ƙara tabbatar da cewa Jami’ar zata ji daɗi tare da yaba irin karimcin da al’umar Babura ke da shi.

A wannan gaɓa ne, Gwamna Badaru yayi kira ga ɗaukacin al’umar Babura masu daraja, da al’umar yankin Jigawa ta Arewa maso Yamma da sauran al’umar Jihar Jigawa su yiwa Jami’ar kyakkyawar tarba da mutuntawa tare da bata haɗin kai domin saka wannan alheri da aka yi musu, da kuma assasa harsashin cigaban da Jami’ar zata samar ga ƴan asalin Ƙaramar Hukumar Babura, da ma waɗanda ba ƴan Ƙaramar Hukumar ba, har ma al’umar dake maƙwabtaka da Ƙasar nan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: