Gwamnatin Tarayya Ta Ƙwace Rigunan Nono Guda 125 Tare Da Rigunan Bacci Mallakar Diezani

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Aliyu Adamu Tsiga
Gwamnatin tarayya ta fara shirin tantance kadarorin wasu mutane da aka fallasa a siyasance, ciki har da tsohuwar ministar albarkatun man fetur, Diezani Alison-Madueke.

Kadarar Diezani dake a Highbrow Banana Island Foreshore Estate, Ikoyi, Legas, ta haɗa da gidaje 18 da kuma ƙarin wasu gidaje shida dake Gini na 3, Block B, Bella Vista, Plot 1, Zone N, Layout na Gwamnatin Tarayya.

Wasu fitattun kadarori da aka lissafa sun haɗa da na tsohon hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Air Chief Marshal Alex Badeh, wanda aka ƙwace gidajensa a unguwannin Wuse 2 da Maitama a Abuja. Sun haɗa da No.14 Adzope Crescent, 19 Kumasi Crescent, Wuse 2; da 6 Umme Street, Wuse 2.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 906

Sauran kayan da aka ƙwato sun haɗa da rigunan nono guda 125, kananan riguna guda 13, da sarƙar jigida guda 41, fulawa mai kauri 73, kwat da wando 11, rigunan bacci guda 11, mayafi 73, da ƙarin wasu rigunan nono guda 30. da kan fanfo guda biyu 2. Fakiti shida na barguna, bargon tebur ɗaya da takalmi guda 64.

A makon da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta fara aikin tantance wasu ƴan kasuwa 613 masu zaman kansu da ake sa ran za su gudanar da siyar da kadarorin da ake zargin an samu ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda a halin yanzu an ƙwace su na dindindin a kusan wurare 25 a faɗin ƙasar.

Adadin kadarorin da aka yi gwanjon su a faɗin ƙasar ya kai 1,620, waɗanda suka haɗa da motoci, gidaje, wayoyi, kwamfiyuta tafi-da-gidanka, tasoshin ruwa da sauran kayayyaki masu daraja. Legas ce ke kan gaba wajen yin gwanjon kadarorin da suka haɗa da gidaje 31 da motoci 589.

A ƙarshen wa’adin, kamfanoni 284 ne suka gabatar da buƙatar tantance kadarorin da aka ƙwace waɗanda suka haɗa da filaye, wuraren kasuwanci, cibiyoyi da filayen da ba a bunƙasa su ba.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.